Kayi Mana Komai a Borno, Dole Mu Zaɓe Ka -Zulum Ga Tinubu
- Gwamnan jihar Borno ya bayyana Tinubu a matsayin wanda ya taimakawa jihar matuƙa gaya
- Gwamna Zulum yace yanzu lokaci na mayar da biki ga Tinubu wanda ya nuna kulawar sa sosai ga jihar
- Tinubu yayi wa al'ummar jihar Borno wani muhimmin alƙawari idan ya ɗare kujerar shugaban ƙasa
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu, ya taimakawa jihar lokacin da take fama da ta'addancin Boko Haram.
Da yake magana a ranar Asabar s wurin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a jihar, gwamnan ya yabawa Tinubu bisa zaɓar Kashim Shettima a matsayin mataimakin sa. Rahoton The Cable
Zulum ya bayyana Tinubu a matsayin wani aminin jihar Borno a siyasance, wanda ya nuna kulawar sa sosai ga jihar a lokacin da take da buƙatar hakan.
"Kayi mana komai yanzu lokaci ne da zamu kawowa APC jihar Borno. Tinubu ya wuce matsayin abokin mu ta fuskar siyasa domin yafi kowa taimakawa jihar Borno lokacin da rikicin Boko Haram yayi ƙamari." A cewar sa
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ya nuna mana kulawa lokacin da abubuwa suka yi mana tsauri. Ya kawo mana ziyara aƙalla sau bakwai ko takwas a cikin shekara 11 da suka gabata. Babu wanda ya taɓa yi mana irin wannan halaccin."
A nasa ɓangaren, Tinubu yace zai farfaɗo da neman man fetur da ake yi a tafkin Chadi, da kuma bunƙasa tafkin domin samar da ayyukan yi da haɓɓaka noma a yankin. Rshoton Vanguard
“Tsaro shine abinda muka fi ba muhimmanci sannan Najeriya zata samu zaman lafiya da daidaito. Mutanen Borno da makwabtan su za su samu cigaba da farin ciki," A cewar sa
"Zulum alama ce ta cigaba. Shettima misali ne na samun nasara."
Haba Baba: Gwamnan APC Ya Bi Hanyar Lalama, Ya Aikawa Buhari Wasika kan Canza Kudi
A wani labarin na daban kuma, gwamnan APC ya saduda ya bi hanyar lalama wajen roƙon shugaba Buhari kan sauya fasalin kuɗi.
Gwamnnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya roƙi shugaba Buhari da ya haƙura ya bari tsofaffin kuɗi su cigaba da aiki, rage raɗaɗin da ƴan Najeriya suke ciki a halin yanzu.
Asali: Legit.ng