Ka Tsaya Wa Borno a Lokacin Wuya, Gwamna Zulum Ya Yabawa Tinubu a Ralin APC

Ka Tsaya Wa Borno a Lokacin Wuya, Gwamna Zulum Ya Yabawa Tinubu a Ralin APC

  • Gwamnan Borno ya yaba wa Bola Ahmed Tinubu a wurin ralin yakin neman zaben APC da ya gudana a jihar ranar Asabar
  • Farfesa Babagana Umaru Zulum yace lokacin da Boko Haram ke kan ganiyarta babu wanda ya tsaya wa Borno kamar Tinubu
  • Tsohon gwamnan Legas ya yi alƙawarin ci gaban da aikin nemo rijiyoyin man Fetur a tafkin chadi idan ya ci zaɓe

Borno - Farfesa Babagana Zulum, gwamnan jihar Borno yace ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar APC, Bola Tinubu, ya nuna wa jihar goyon baya gagara misali lokaci ƙangin Boko Haram.

Jaridar The Cable ta rahoto cewa gwamna Zulum ya bayyana haka ne a wurin ralin kamfen jam'iyyar APC da ya gudana a Borno jiya Asabar.

Ralin APC.
Ka Tsaya Wa Borno a Lokacin Wuya, Gwamna Zulum Ya Yabawa Tinubu a Ralin APC Hoto: Babagana Zulum/Facebook
Asali: Facebook

A ruwayar The Nation, Farfesa Zulum ya yabawa Asiwaju bisa ɗaukar Sanata Kashim Shettim, tsohon gwamnan jihar a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

2023: Zulum Ya Yabawa Tinubu, Yayi Masa Wani Muhimmin Alƙawari

A wata sanarwa da ofishin yaɗa labaran gwamna, an haƙaito Zulum na cewa Tinubu makunsancin Borno ne na kusa a siyasa, wanda ya nuna, "Damuwa ga jihar lokacin da ta shiga ƙaƙanikayi."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ka mana komai kuma yanzu lokaci ya yi da zamu maida biki. Tinubu ya zarce a kira shi da aminin Borno domin ya nuna damuwarsa ga jihar fiye da kowa lokacin da Boko Haram ke kan ganiyarta."
"A lokacin da muke cikin ƙangin wahala, a koda yaushe yana tare damu, ya zo nan ziyara sama da sau 7 zuwa takwas a shekaru 11 da suka shige. Babu wanda ya kwatanta haka."

- A cewar Zulum.

Tinubu ya ɗauki alkawurra

Da yake nasa jawabin, Bola Tinubu ya ce zai farfaɗo da haƙo ɗan mai a tafkin Chadi kuma zai sabunta kogin domin haɓaka noma da samar da ayyukan yi.

Kara karanta wannan

"Muhimman Abu 5" Abinda Atiku Ya Bayyana Wa Yan Najeriya a Wurin Kamfen PDP Na Karshe Gabanin Zabe

"Tsaro ne a farkon kudirorin mu kuma nan gaba Najeriya zata zauna lafiya, farin ciki da kwanciyar hankali zai dawo wa mutanen Borno da makotan jihohi."

"Gwamna Zulum alama ce ta ci gaba, haka zalika Kashim Shettima wakilin nasarori ne," inji Tinubu.

Arewa Maso Gabas Zata Girgiza Atiku a Zaɓe Mai Zuwa, Jigon APC

A wani labarin kuma Babban Jigon APC ya ce ba wahalar da zata hana mutanen Borno da arewa maso gabas zaɓen Tinubu/Shettima

Mataimakin jami'in hulɗa da jama'a na jam'iyar APC ta ƙasa, Murtala Ajaka, yace taron Borno alama ce babba kuma sako ne kai tsaye ga PDP da Atiku Abubakar.

A cewarsa wahalar karancin takardun naira ba zata dakatar da mutanen arewa maso gabas fitowa su jefa wa jam'iyyar APC kuri'unsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262