Muna Nan Daram a PDP, Gwamna Wike Ya Musanta Jita-Jitar Zai Koma APC
- Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya jaddada biyayyarsa da mubaya'a a matsayin mamban Peoples Democratic Party (PDP)
- Wike ya bayyana haka ne a wurin wani tattaunawa tare da manema labarai ranar Alhamis, 16 ga watan Fabrairu, 2023
- Gwamna Wike ya bayyana waɗanda suka gudu kuma suka dawo PDP a lokutan baya da 'yan fashin teku'
Rivers - Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya kore duk wani tunanin cewa wata rana zai fice daga jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).
Gwamnan ya yi wannan furucin ne ranar Alhamis, 16 ga watan Fabrairu, 2023 a gidansa da ke Patakwal, yayin zantawa da yan jarida wanda Legit.ng Hausa ta bibiya.
Ya yi bayanin cewa yana nan daram kamar yadda aka san shi a matsayin mamba mai biyayya kuma ba zai taɓa guduwa daga PDP ya barta hannun waɗanda suka tsere sannan suka dawo ba.
A kalamansa, gwamna Wike ya ce:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Ina nan daram a cikin jam'iyya, ma fi yawan waɗan can da kuke gani duk sun taɓa guduwa daga PDP. Shin bana faɗa maku ba a baya ba zamu taba barin jam'iyar nan ba?"
"Muna nan komai rintsi a cikin wannan jam'iyyar kuma zamu ci gaba da yaƙin da muke yi, ba zamu bar jam'iyyar nan ba, idan mun tafi mu barta hannun wa? Mu barta hannun waɗanda suka gudu a baya? Yan fashi, ba zamu yi haka ba."
"Muna nan a wannan jam'iyyar wata rana zasu sake guduwa su dawo, mu dai muna nan daram."
Tinubu ya cancanci zama shugaban kasa - Wike
Baya ga haka gwamna Wike ya bayyana cewa ɗan takarar shugaban kasa a inuwar APC, Asiwaju Bola Tinubu, yana da duk abinda ake bukata na mulkar Najeriya.
Wike ya faɗi haka ne yayin da ya karbi bakuncin Tinubu, Shettima da sauran yan tawagarsa bayan sun kammala kamfe a jihar Ribas ranar Laraba.
A wani labarin kuma Gwamna Wike Ya Kore Yuwuwar Sulhu Tsakanin G5 da Atiku Gabanin Zaɓen 2023
Gwamnan Ribas kuma jagoran G-5 ko kaɗan ba zai sake zama da wani mamban PDP daga tsagin Atiku Abubakar ba da nufin neman sulhu.
A cewar Wike lokaci ya riga ya kure kuma sun faɗi haka, a yanzu babu wanda zai iya dakatar da su.
Asali: Legit.ng