Duk Wanda Ya Ci Kuɗina Bai Zabeni Ba Zai Mutu, Dan Takarar Gwamnan PDP
- Mai neman zama gwamnan Neja a jam'iyyar PDP, Isah Liman Kantigi, ya gargaɗin masu shirin cin amanarsa a zaɓen 2023
- Ɗan siyasan ya bayyana abinda mutum zai girba matukar ya karbi kudinsa amma bai dangwala masa kuri'a ba
- A watan Maris mai zuwa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa ta shirya gudanar da zaɓen gwamnoni a Najeriya
Niger - Ɗan takarar gwamnan jihar Neja a inuwar Peoples Democratic Party (PDP), Isah Liman Kantigi, ya gargadi masu shirin karban kuɗinsa kuma su ƙi jefa masa kuri'a ranar zaɓe.
Jaridar Leadership ta tattaro cewa an jiyo Kantigi yana isar da wannan gargadi ga magoya bayansa a wani bidiyo da ke yawo a soshiyal midiya.
A cikin Bidiyon an ji ɗan takarar na cewa duk wanda ya sake ya lamushe kuɗinsa kuma ya ƙi mara masa baya a zaben gwamnoni mai zuwa a watan Maris to ya yi bankwana da duniya.
Liman Kantigi, ya sanya fararen kaya da farar hula kuma yana kan Babur mai ƙafa uku watau Nafep lokacin da ya yi wannan gargaɗin a Bidiyon dake yawo.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Da yake magana cikin Ingausa, watau turanci da Hausa a haɗe, ɗan takarar gwamnan Neja a inuwar PDP, Isah Liman Kantigi, ya bayyana yadda wanda ya ci masa kuɗin zai kare.
Ya ce duk mutumin da ya karɓi kuɗinsa bai zaɓe shi ba zai fara ganin sabbin mafarkai, daga nan kuma zai fara aman Kumfa har rai ya yi halinsa.
"Idan na baka kuma ka cinye, zaka fara wasu mafarkai, sannan ka fara amai na kumfa daga nan kuma a haka rai zai yi halinsa," inji shi yayin da yake gargaɗinsu.
Punch ta rahoto cewa Kantigi ya kasance tsohon shugaban ƙaramar hukumar Edati kuma tsohon kwamishinan kananan hukumomi a zamanin mulkin Muazu Babangida Aliyu.
Shin Mutane Sun Yi Asara Kenan? Matakai 3 da Zaku Bi Ku Maida Tsoffin Naira Banki Duk da Wa'adi Ya Cika
A kwanakin baya ya sha yabo sa'ilin da ya ba da tallafin Na'urorin ajiyar wuta wato Transformer guda biyu ga al'ummar yankin Dangana da Duma a karamar hukumar Lapai.
Maganar Sulhu ta kare a PDP - Wike
A wani labarin kuma Gwamna Wike Ya Kore Yuwuwar Sulhu Tsakanin G5 da Atiku Gabanin Zaɓen 2023
Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya ce lokaci ya ƙare tawagar G-5 ba zata sasanta da Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban kasa na PDP ba. Gwamnan ya ce ba wanda ya isa ya sake ganawa da shi kan rikicin PDP domin suna ganin zasu iya kai labari ko da babu gwamnomin G-5.
Asali: Legit.ng