Shugaban Kasa a 2023: Bana Yi Maka Kamfen Kuma Bana Adawa Da Kai – Wike Ga Tinubu
- Gwamnan jihar Ribas ya bayyana matsayinsa na karshe a kan dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu
- Yayin ziyarar da kwamitin kamfen din APC ta kai gidan gwamnatin jihar Ribas a ranar Laraba, Wike ya bayyana matsayinsa cewa baya goyon bayan Tinubu kuma baya adawa da shi
- Wike ya kuma bayyana cewa Tinubu na da cancantar da ake bukata daga wajen shugaba don jagorantar Najeriya
Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya bayyana matsayinsa kan goyon bayansa ga dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
A ranar Laraba, 15 ga watan Fabrairu lokacin da ya tarbo tsohon gwamnan na jihar Lagas da tawagar kamfen dinsa a Port Harcourt, Wike ya ce shi baya yi wa Tinubu aiki haka kuma baya adawa da shi.
CBN: Tinubu Ya Gabatar Da Babban Bukata 1 Bayan An Yi Zanga-Zanga Kan Karancin Naira a Fadin Najeriya
A karshe Wike ya bayyana matsayinsa kan Tinubu
A wani bidiyo da ke yawo a intanet, Wike ya bayyana cewa ya zama dole a fadi gaskiya kuma cewa Tinubu yana da duk abun bukata don shugabantar kasar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Gwamnan na jam'iyyare PDP, ya kuma bayyana cewa baya farin ciki da yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ke tafiyar da lamarin karancin kudi a kasar, da kuma yadda shuban Babban Bankin CBN ke kin bin umurnin kotun koli na amfani da tsoffin naira.
Kalli bidiyon a nan:
Tinubu ya roki yan Najeriya da su guji tashin hankali kan karancin Naira
A wani labarin kuma, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya nuna takaicinsa kan tashe-tashen hankula da aka samu a kasar sakamakon rashin wadatuwar sabbin takardun Naira da kuma kin karbar tsoffin kudi da ake.
Tinubu ya bukaci al'ummar kasar da su kara hakuri yayin da gwamnatin tarayya da na jiha ke aiki ba ji ba gani don ganin ta magance mawuyacin halin da manufar sauya kudi na CBN ya haifar ga yan kasar.
Ya kuma ce babban abun da yakamata mutane su mayar da hankali a kai shine lamarin babban zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu da ke kara gabatowa maimakon tashe-tashen hankali a yankunan su.
Asali: Legit.ng