Bamu Da Kuɗin Da Zamu Gudanar Da Zaɓe a Hannun Mu -INEC Ta Koka

Bamu Da Kuɗin Da Zamu Gudanar Da Zaɓe a Hannun Mu -INEC Ta Koka

  • Hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta koka kan rashin samun kuɗaɗe duk da ana saura kwanaki kaɗan a fara zaɓe a Najeriya
  • Hukumar INEC ta buƙaci CBN da ya sassauta kan wasu sharuɗɗa da ya gindaya wajen cirar kuɗi
  • Rashin tsaɓar kuɗaɗe a hannun hukumar INEC ka iya kawo babbar tawaya ga babban zaɓen dake tafe

A yayin da ya rage saura kwanaki 10 a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisar wakilai, har yanzu ba a samarwa hukumar zaɓe ta INEC kuɗin da zata rabawa ma'aikatan zaɓe na wucin gadi ba. Rahoton Daily Trust.

Shugaban hukumar zaɓen mai zaman kanta (INEC) Farfesa Mahmood Yakubu, a ranar Talata data gabata ya gana da babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, inda ya nemi bankin wata alfarma.

Kara karanta wannan

2023: Hantar Atiku Ta Kaɗa, Gwamna Wike Ya Faɗi Abinda Gwamnonin G-5 Zasu Yi Ranar Zaɓe

Mahmood Yakubu
Bamu Da Kuɗin Da Zamu Gudanar Da Zaɓe a Hannun Mu -INEC Ta Koka
Asali: UGC

Mahmood ya buƙaci CBN da ya ɗaga ƙafa kan wasu ƙaidojin cirar kuɗi da ya gindaya da kuma buƙatar samar da tsabar kuɗi saboda wasu abubuwan da ba za a iya tura kuɗi domin su ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A yayin da yake nasa jawabin, Emefiele, yace zai tabbatar da cewa bankin bai zama silar kawo tangarɗa ba ga zaɓen dake tafe, inda ya tabbatar da cewa za a samarwa da INEC kuɗin da take buƙata.

Sai dai, alamu sun nuna cewa har yanzu hukumar bata samu kuɗaɗen ba, hakan ya bayyana bayan da kwamishinan hukumar na birnin tarayya Abuja, Alhaji Yahaya Bello, yayi magana kan lamarin.

Bello ya bayyana cewa sabon shirin CBN na taƙaita kuɗi a hannun jama'a ka iya kawo naƙasu ga hukumar INEC wajen gudanar da zaɓe.

Kara karanta wannan

Shin karancin Naira zai shafi zaben bana? Jami'in INEC ya yi gargadi mai daukar hankali

A kalamansa:

"Kafin ranar zaɓe, zamu tura mutanen d za suyi mana aiki. A daren ranar Juma'a (kwana ɗaya kafin zaɓe, a birnin tarayya Abuja muna da sama da ma'aikatan wucin gadi 12,000 da zamu basu kuɗi."
“Duk cikin su ba wanda zai karɓi wani abu idan ba tsaɓar kuɗi ba. Ina maganar mutum 12,000 kawai a birnin tarayya waɗanda kowanen su na buƙatar samun tsaɓar kuɗi na N5,000 a daren ranar Juma'a.
Sannan kuma suma waɗanda zasu ɗauki mutanen mu, kayan aiki da jami'an tsaro zuwa rumfunan zaɓe, suna buƙatar tsaɓar kuɗi.
“Haka kuma, ba zai yiwu ba ka kai jami'an tsaro rumfar zaɓe ba tun safiya har zuwa yamma, ba tare da an bashi kuɗin da zai ci abinci ba, sannan ba zai yiwu kayi tsammanin cewa zai je POS ya ciro N1,000 da zaka ba shi ba."

Sai dai, ya tabbatar da cewa hukumar zaɓe ta INEC na tattauna da CBN domin ganin ta yadda za a magance matsalar.

Kara karanta wannan

Shin Mutane Sun Yi Asara Kenan? Matakai 3 da Zaku Bi Ku Maida Tsoffin Naira Banki Duk da Wa'adi Ya Cika

Asali: Legit.ng

Online view pixel