Juyin Mulki: Fani-Kayode Ya Bar Hannun DSS, Ya Lissafo Wadanda Suka Taimaka Wajen Fitowarsa
- Femi Fani-Kayode, daraktan sadarwa na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC, ya nuna nadama kan fargabar da ya nuna cewa ana shirin yin juyin mulki
- Bayan kokawar da ya yi, hukumar DSS ta gayyace shi sannan ta yi masa tambayoyi na sama da awanni 5 a ranar Litinin, 13 ga watan Fabrairu
- Bayan an sake shi, tsohon ministan ya ce kamata ya yi ace ya yi nazari kafin ya bayyanawa jama'a lamarin
- Fani-Kayode ya yi godiya ga dukkanin shugabannin APC, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar, Bola Tinubu, yayin da aka bukaci ya dawo ofishin DSS a ranar Laraba
Abuja - Femi Fani-Kayode, daraktan sadarwar zamani na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ya nuna nadama kan kokawa da ya yi game da yunkurin yin juyin mulki a kasar.
Bayan hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta tasa shi gaba na kimanin awanni biyar, ya ce da kamata ya yi ace ya lura da kyau kafin fallasa zancen ga jama'a, jaridar The Guardian ta rahoto.
FKK ya yi danasani kan kokawa da ya yi game da yunkurin yin juyin mulki
Ya yarda cewa batun juyin mulkin ya tayar da kura a fadin siyasar kasar yayin da ya yi bayanin cewa manufarsa na yin hakan shine don tabbatar da ganin cewa hukumomin tsaro sun zama cikin shiri koda zai zamana akwai kamshin gaskiya a lamarin.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Yayin da yake jaddada cewar bai aikata laifin komai ba, Fani-Kayode ya yarda cewa da ya dauki lamarin ta siga daban, jaridar Premium Times ta rahoto.
Tsohon ministan sufurin jiragen saman ya bayyana cewa ya amsa gayyatar DSS ne saboda hannunsa a tsaftacce suke kan lamarin
Ya kuma jadddada cewa an umuce shi da ya dawo hedkwatar rundunar a ranar Laraba, 15 ga watan Fabrairu, kafin a yanke hukunci kan ko za a kai shi kotu ko a jingine lamarin.
Fani-Kayode ya mika godiyarsa ga shugabannin APC
A safiyar ranar Talata, 14 ga watan Fabrairu, FKK kamar yadda ake masa inkiya, ya je shafinsa na Twitter don nuna godiya ga dukkanin wadanda suna nuna damuwa game da gayyatar da DSS suka yi masa.
Ya yi godiya ga Bola Tinubu da Kashim Shettima, dan takarar shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa na APC, shugaban jam'iyyar na kasa, Abdullahi Adamu da darakta janar na kwamitin yakin neman zaben APC, Simon Lalong da dukkanin tawagar kamfen din.
Atiku: Hedkwatar tsaro ta magantu kan zargin yunkurin juyin mulki a 2023
A baya mun ji cewa hedkwatar tsaro ta yi Allah wadai da rade-radin da ake yadawa cewa Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na PDP ya hada kai da wasu sojoji don yin juyin mulki a zaben 2023.
Da take karyata batun, DHQ ta ce tana mutunta damokradiyyar Najeriya kuma za ta gayyaci wadanda suka yada zargin.
Asali: Legit.ng