Wike Ya Goyi Bayan Tinubu? Gwamnan Ribas Ya Amince Dan Takarar APC Ya Yi Taro Kyauta A Filin Wasa

Wike Ya Goyi Bayan Tinubu? Gwamnan Ribas Ya Amince Dan Takarar APC Ya Yi Taro Kyauta A Filin Wasa

  • Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya amince a bada filin wasa na Yakubu Gowon da ke Elekahia don kamfe din takarar shugabancin kasa na Bola Tinubu
  • Wike ya amince da bada filin wasan ga APC ba tare da karbar naira miliyan 5 da ya ambata a doka jihar ba
  • Ana shirin yin taron yakin neman zaben na dan takarar shugaban kasa na APC a Ribas din ne a ranar Laraba 15 ga watan Fabrairu karlashin jagorancin Tony Okocha

Fatakwal, Jihar Ribas - Gwamna Nyesom Wike ya amince wa jam'iyyar All Progressives Congress, APC, amfani da filin wasanni na Yakubu Gowon da ke Elekahia don kamfen din Asiwaju Bola Tinubu.

Shugaban kamfen din Bola Tinubu, Tony Okocha ne ya bayyana hakan, a yayin zantawa da ya yi da manema labarai a Fatakwal a ranar Laraba 8 ga watan Fabrairu, The Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Takarar Shugaban Kasa: Mai Goyon Bayan Atiku, Reno Omokri Ya Soki Peter Obi, Ya Yaba Wa Bola Tinubu

Nyesom Wike
Wike Ya Goyi Bayan Tinubu? Gwamnan Ribas Ya Amince Dan Takarar APC Ya Yi Taro Kyauta A Filin Wasa. Hoto: The Guardian
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Okocha ya kara da cewa Gwamna Wike ya bada filin wasan ba tare da karbar naira miliyan 5 na haya da ke dokar kwamitin kamfe na 21, rahoton Guardian.

Ya kara da cewa an kammala shiri don tabbatar da yin taron lami lafiya a ranar Laraba 15 ga watan Fabrairu.

Okocha ya ce:

"Wike bisa karamcinsa ya amince ya bada wani wurin taron, filin wasa na Yakubu Gowon a Elekahia, Fatakwal, don taron kamfen din shugaban kasa da za a yi a ranar 15 ga watan Fabrairun 2023 ba tare da karbar ko sisi ba."

An kafa kwamiti don tabbatar da nasarar taron kamfe a Jihar Ribas - Okocha

Da ya ke cigaba da jawabi, Okocha, wanda shine shugaban kungiyar Bola Ahmed Tinubu (BAT-Vanguard a Kudu maso Kudu), ya ce an kafa kwamiti na mutum 11 don kula da tabbatar da nasarar taron a jihar.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Na San Yadda Zan Yadda Zan Gyara Tattalin Arzikin Najeriya, Bola Tinubu

Ya ce kwamitin ta zauna ta kuma yi aikinta don ganin an yi taron cikin nasara kuma Tinubu ya ci zabe.

Zaben 2023: Ku hakura ku janye wa Makinde takara, Gwamna Wike ya nemi alfarma daga dan takarar APC

A baya kun ji cewa Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya yi roko ga yan takarar gwamna na jam'iyyun adawa a jihar Oyo su hakura da yin takara a 2023.

Cikin wadanda Wike ya roka har da Sen Teslim Folarin, dan takarar gwamnan jihar Oyo karkashin jam'iyyar All Progressives Congress, APC a zaben na shekarar 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164