Wasu Mutanen a Aso Villa Suna Yi Wa Atiku Aiki, Fani Kayode

Wasu Mutanen a Aso Villa Suna Yi Wa Atiku Aiki, Fani Kayode

  • Tsohon ministan sufurin jiragen sama kuma babban jigon APC ya tona asirin mutanen fadar shugaban kasa dake tare da Atiku
  • Femi Fani-Kayode, Daraktan midiya ns kwamitim kamfen Tinubu/Shettima yace sabbin tsarukan da CBN ya zo da su akwai ayar tambaya
  • Wannan na zuwa ne awanni kalilan bayan gwamnan Kaduna, Malam El-Rufai, yace akwai masu yaƙar Tinubu a kusa da Buhari

Daraktan Midiya na kwamitin yakin neman zaben APC, Femi Fani-Kayode, ya yi ikirarin cewa akwai wasu mutane a fadar shugaban kasa dake wa Atiku Abubakar aiki.

Fani-Kayode ya yi wannan furucin ne yayin hira a gidan talabijin Channels tv a shirinsu mai suna Politics Today sa'ilin da yake tsokacin kan kalaman gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai.

Femi Fani Kayode.
Wasu Mutanen a Aso Villa Suna Yi Wa Atiku Aiki, Fani Kayode Hoto: FFK

Tun da fari, gwamna Malam Nasiru El-Rufai ya ce akwai wasu mutane a Aso Rock da suke aikin yaƙar dan takarar shugaban kasa a inuwar APC, Asiwaju Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Aisha Buhari Ta Gaskata El-Rufai Kan Markashiyar Da Ake Kitsawa Tinubu a Fadar

Da yake ɗorawa kan waɗan nan kalaman a rahoton Daily Trust, Fani-Kayode ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Duk waɗan nan abubuwan dauke hankalin na damuwa ne saboda muna aiki tukuru amma wasu na kokarin kawo mana tangarɗa a hanyar da muka kama da nufin gurɓata miƙa mulki.
"Ni a tunani na akwai wasu mutane da suke wa ɗan takarar shugaban kasan da nake kallo a karamin alhaki kamar Atiku."

Tsarin sauya takardun naira

Fani-Kayode, tsohon ministan sufurin jirgane sama ya bayyana cewa sabbin tsarukan da gwamnan babban banki CBN, Godwin Emefiele, ya kirkiro suna da alamar tambaya.

"Akwai alamar tambaya a sabbin tsarukan da gwamnan CBN ya zo da su. Bana ja da tsarin amma lokacin da aka tsiro da shi."
"Mutane na wahala, suna shan azaba, ba zasu cimma komai ba, amma ka duba abinda aka masu."

Kara karanta wannan

2023: Wasu Masu Son Gaje Buhari Abin Dariya Ne, Gwamnan Arewa Ya Tabo 'Yan Takarar Shugaban Kasa

Ban Taba Cewa Zan Fito Gaban Kamara Na Fadi Wanda Zan Goyi Baya Ba, Wike

A wani labarin kuma Gwamna Wike ya maida martani yayin da ake ta guna-gunin bai faɗi ɗan takarar da zai marawa baya ba

Gwamnan ya ce babu inda aka ji ya sanar da 'yan Najeriya ga hanyar da zai bi wajen ayyana wanda zai marawa baya ya zama shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262