Miyagu Sun Sace Darektan Yakin Neman Zaben Jam’iyyar APC a Wajen Yawon Kamfe
- An yi awon gaba da Darektan yakin neman zaben Gwamnan APC a karamar Opobo/Nkoro Opobo
- Tony Cole ya ce wasu ‘yan iskan gari suka shigo wajen kamfe, suka dauke Boma Brown a makon nan
- Ganin abubuwan da ke faruwa, Jam’iyyar APC ta bukaci canza kwamishinan ‘yan sandan jihar Ribas
Rivers- Jam’iyyar APC ta reshen jihar Ribas, ta bada sanarwar cewa an sace mata Darektan yakin kamfen na karamar hukumar Opobo/Nkoro Opobo.
Rahoton Punch na ranar Talata, ya nuna ana zargin ‘yan daban siyasa sun yi awon gaba da Boma Brown ne a wajen wani taron kamfe da aka shirya.
Jam’iyyar APC mai hamayya a Ribas ta zargi jami’an ‘yan sanda da sakaci a kan abin da ya faru, ta ce ya kamata a ce rundunarsu na nan a wajen taron.
A jiya ne Tonye Cole mai neman zama Gwamnan jihar Ribas a karkashin APC ya shaidawa manema labarai yadda wannan mummunan abin ya faru.
'Yan dabar siyasa sun kutso da makamai
Tonye Cole ya ce ‘yan iskan gari sun shigo inda jam’iyyar APC ta ke kamfe, daga nan su ka fara harbe-harbe ko ta ina, ana haka ne suka dauke Brown.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
‘Dan takaran ya yi kira ga gwamnati ta sa dokar ta-baci saboda bangar siyasa da ya kazanta a Ribas.
Darlington Nwauju wanda shi ne Sakataren yada labaran APC na reshen jihar Kudu maso kudancin kasar ya tabbatar da aukuwar lamarin, yana yin tir.
Mista Nwauju ya kira lamarin da dabbanci a siyasa, amma kuma ya bayyana cewa Cole da Dr. Dakuku Peterside sun taimaka har an kubutar da Brown.
Akwai bukatar canza CP - APC
This Day tace Kakakin kwamitin yakin neman zaben Gwamna a jihar Ribas, Sogbeye Eli, yana so ne a canza kwamishinan ‘yan sanda watau Okon Effiong.
Ganin irin kazamar siyasar da ake yi, Eli yana ganin Effiong ya sa wasa a aikinsa, don haka a madadin APC ya nemi a canza shi da wani kwamishinan.
Kwamitin yakin zaben APC ya ce irin haka ya faru a wajen kamfen Dumo Lulu-Briggs da Sanata Magnus Abe da suke takarar Gwamna a Accord da SDP.
Takarar Muhammad Sani Sha’aban
Idan aka koma siyasar Arewacin Najeriya, za a ji labari Muhammad Sani Sha’aban ya bude yakin neman takarar Gwamna a inuwar Action Democratic Party.
Kwanaki ‘Dan siyasar da aka kafa APC da shi a Kaduna ya bar Jam’iyyar zuwa ADP. Sha’aban ya ce zai yaki talauci da rashin tsaro idan har ya zama Gwamna.
Asali: Legit.ng