Kujerar Sanatan Kebbi: Aliero Zai Gwabza da Bagudu Yayin da Kotun Koli Ta Tabbatar da Shi Dan Takarar PDP
- Kotu ta tabbatar da Adamu Aliero a matsayin sahihin dan takarar sanatan Kebbi ta tsakiya karkashin inuwar jam'iyyar PDP
- Kotun koli ta zartar da hukunci inda ta soke hukuncin kotun daukaka kara na ayyana Saidu Haruna a matsayin dan takarar PDP
- Za a fafata tsakanin Aliero da gwamnan jihar Kebbi mai ci, Atiku Bagudu wanda ke takarar kujerar a APC
Kotun koli ta tabbatar da Sanata Muhammad Adamu Aliero a matsayin dan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na sanaa mai wakiltan yankin Kebbi ta tsakiya, jaridar Daily Trust ta rahoto.
A ranar Litinin ne kwamitin mutum biyar karkashin jagorancin Justis China Centus Nweze ya jingine hukuncin kotun daukaka kara, wacce ta fara jingine karar da Aliero ya daukaka inda yake kalubalantar hukuncin babbar kotun tarayya kan zaben fidda gwanin jam'iyyar.
Da suke yanke hukunci, Kwamitin alkalan karkashin jagorancin Justis Amina Augue, sun ce karar da Aliero ya daukaka yana mai kalubalantar ayyana Saidu Haruna a matsayin dan takarar PDP na kujerar sanata na bisa daidai.
Hakazalika, babban kotun ta tabbatar da zaben Dr Abubakar Yahaya Abdullahi a matsayin dan takarar PDP na sanata mai wakiltan Kebbi ta arewa a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Za a fafata tsakanin Sanata Aliero na PDP da Gwamna Bagudu na APC
Aliero zai gwabza da Gwamna Atiku Bagudu, wanda ke takarar kujerar sanata mai wakiltan Kebbi ta tsakiya a karkashin inuwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), rahoton Aminiya.
Akwai yiwuwar Kwankwaso ya koma bayan Atiku a zabe mai zuwa, Jigon arewa
A wani bari na daban, hasashe sun nuna cewa dattawa, sarakuna na manyan masu ruwa da tsaki a yankin arewacin kasar sun fara tattaunawa da Sanata Rabiu Kwankwaso game da yadda zaben shugaban kasa na 2023 za ta kasance.
Wani jigon arewa da aka sakaya sunansa ya ce wannan tattaunawar yunkuri ne na lallashin Kwankwaso tare da shawo kansa kan ya janye sannan ya yi hadaka da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar.
An yanke wannan shawara ce duba ga yadda tsagin gwamnonin G-5 karkashin jagorancin Gwamna Nyesom Wike suka taso Atiku a gaba.
Asali: Legit.ng