2023: Za Ku Yi Nadama Idan Ba Ku Zabe Ni Ba, Dan Takarar Gwamna Na APC Ya Fada Wa Wata Kabila A Jiharsa

2023: Za Ku Yi Nadama Idan Ba Ku Zabe Ni Ba, Dan Takarar Gwamna Na APC Ya Fada Wa Wata Kabila A Jiharsa

  • Dan takarar Gwamnan Jihar Ebonyi na APC ya bayyana wa wata kabila da su tabbatar sun zabe shi
  • Nwifuru ya gargadi kabilar Ezza da za su yi matukar nadama in ba su zabe shi ba a zaben 2023
  • Ya musu alkawarin in suka zabe shi zai shige gaba a bawa dan kabilar takara a 2031 bayan kammala wa'adinsa

Ebonyi - Dan takarar Gwamnan Jihar Ebonyi a jam'iyyar APC a Jihar Ebonyi, Rt. Hon. Francis Nwifuru, ya shawarci yan kabilar Ezza da su zabe ranar zaben 19 ga watan Maris ko su yi nadama.

Ya yi gargadin ne a wajen taron yakin neman zabe a Onueke, hedikwatar Karamar Hukumar Ezza South da ke jihar, ranar Juma'a, rahoton Daily Trust.

Ezzra
2023: Za Ku Yi Nadama Idan Ba Ku Zabe Ni Ba, Dan Takarar Gwamna Na APC Ya Fada Wa Mutanen Jiharsa. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

"APC Zata Lashe Zabe" Bola Tinubu Ya Fallasa Wata Makarkashiya da Ake Masa Game da Zaben 2023

Akwai 'kishin-'kishin din cewa yan kabilar suna neman goyon bayan yan kabilar Ikwo, don goya wa dan kabilarsu, Prof Benard Odo, na babbar jam'iyyar adawa ta APGA.

Nwifuru, wanda ya shaidawa yan Ezza cewa basu ne ya kamata su jagoranci jihar ba bayan Gwamna David Umahi, ya ce in suka zabe shi, zai bawa yan kabilar takara a 2031.

Ya ce: '

"Ya jama'ar Ezza, ku saurara kuji dalilin da yasa nace zaku yi nadama in baku zabe ni ba saboda a matsayina da na dan gari, na yarda da adalci da daidaito.
''Wannan lokacin ya kamata mu nuna karfi kuma zamu nuna haka ne ta hanyar zabar APC, ba wata gwamnati da zata bada mulki ga kabilar Ezza. Gwamnati na ce kadai, idan kuka zabe ni kwan ku da kwarkwata, kuma na samu kuri'unku dari bisa dari, zanyi magana da manyan masu ruwa da tsaki na jihar mu."

Ya cigaba da cewa:

Kara karanta wannan

Peter Obi Ya Kai Ziyarar Bazata Kudancin Borno, Ya Kafa Tarihi

''Amma idan baku yi haka ba, kada kuyi tsammanin zanyi muku haka, idan muka rasa wata kujera anan zan dauka cewa baku da bukatata kuma baza muyi magana a madadinku ba in lokaci yayi, 2031 ne lokacin ku."

Nwifuru shine kakakin majalisar jihar a halin yanzu.

Daily Trust ta ruwaito cewa gangamin APC ya fara tara jama'a bayan kaddamar da shi wancan satin bayan fitowar tsirarun mutane a Izzi da Ikwo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164