'Kana Bukatar Taimako', Martanin Fadar Shugaban Kasa Ga Kalaman Tanko Yakasai Kan Tinubu
- Fadar shugaban kasa ta mayar da martani kan kalaman da Dattijon Kasa Tanko Yakasai ya yi
- Fadar ta bakin Malam Garba Shehu ta shaidawa yan Najeriya da suyi watsi da kalaman da ta kira na gigin tsufa
- Garba Shehu ya kuma bayyana cewa za a ci gaba da ganin Shugaba Buhari a wurin gangamin yakin neman zaben Tinubu
A ranar Laraba, fadar shugaban kasa ta bukaci 'yan Najeriya da kada su dauki kalaman dattijo, Alhaji Tanko Yakasai, ''da muhimmanci'' dangane da sukar shugaba Buhari kan goyon bayan dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar APC a babban zabe mai zuwa, rahoton Daily Trust.
Babban mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin watsa labarai, Malam Garba Shehu, shi yayi martanin a wata sanarwa mai taken ''dangane da sukar da Alhaji Tanko Yakasai ya yi wa shugaban kasa kan goyon bayan APC a zabe mai zuwa.''
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce dattijon yana bukatar ''a dan taimaka masa'' saboda kalamansa sun ci karo da abubuwan da Shugaba Buhari yake yi a wannan lokacin na yakin neman zabe, ya kuma kara da cewa Shugaba Buhari zai ci gaba da yawon yakin neman zabe a satika masu zuwa.
Ya ce:
''Babu wanda yasan Alhaji Tanko Yakasai a jam'iyyar APC, kowa yana damar yin ra'ayinsa, amma abin da muka sani shine abin da ya fada a hirarsa ta baya-bayan nan ba daga jam'iyya ko fadar shugaban kasa ya fito ba. Goyon bayansa ga Asiwaju Bola Ahmed Tinubu abu ne mai kyau duk da abu ne mai wahala hakan yayi wani tasiri.
''Yana da yancin bayyanan kwarewarsa a matsayinsa na dattijon kasa, jogora a gwamnati kuma wanda yake da ilimi akan alummar Najeriya suna daga sahun gaba na neman kujerar lamba daya."
Ya cigaba da cewa:
''Amma sukar da Yakasai yayi wa Shugaba Buhari ya bar abin tambaya kan abin da shugaban yake yi. A ranar Litinin ne, ya fita yakin neman zabe don nuna goyon baya ga dan takarar jam'iyya. Daga cikin ayyukan da aka sahalewa shugaban, zai sake bayyana a wasu tarukan gangamin yakin neman zabe da za ayi a satuka masu zuwa.
''Goyon bayansa ga takarar jam'iyya Asiwaju Bola Tinubu ba abin suka bane.
''Da ace ba a gidan Talabijin yayi hirar ba, kalaman rashin kan gadon da Yakasai yayi za a iya wofarta dasu a matsayin tuntuben harshe. Amma hirace ta kai tsaye a Talabijin.
''Don gane ga waddannan kalaman nasa kan shugaba Buhari, kada wanda ya dauke su da muhimmanci. Dattijon na cikin yanayi mara dadi kuma yana bukatar a dan taimaka masa.''
Asali: Legit.ng