Miyagu Sun Farmaki Dan Takarar Gwamna a Jihar Ribas, Sun Tafka Barna

Miyagu Sun Farmaki Dan Takarar Gwamna a Jihar Ribas, Sun Tafka Barna

  • Wasu miyagu ɗauke da bindigu sun farmaki dan takarar gwamna na Accord Party a jihar Ribas ranar Asabar 21 ga watan Janairu
  • Chief Dumo Lulu-Briggs, shi ne ya tabbatar da lamarin da kansa, ya ce yana hanyar zuwa Sakatariyar Accord da ya samu labarin an kai hari
  • Ya bayyana cewa yayin da ya yi kokarin kiran lambar wayan kwamishinan 'yan sanda na Ribas ba ta shiga ba

Rivers - Wasu tsageru sun farmaki ɗan takarar gwamna karkashin inuwar jam'iyar Accord Party a jihar Ribas, Chief Dumo Lulu-Briggs, a yankin ƙaramar hukumar Etche ranar Asabar.

Jaridar Tribune Online ta tattaro cewa yayin harin an yi kaca-kaca da motar dan takarar wacce harsashi ba ya iya fasawa.

Chief Dumo Lulu-Briggs.
Miyagu Sun Farmaki Dan Takarar Gwamna a Jihar Ribas, Sun Tafka Barna Hoto: tribuneonline
Asali: UGC

Mista Lulu Briggs da kasa ne ya tabbatar da lamarin, inda ya ce bayan ya samu labarin an kai hari Sakatariyar Accord Party dake garin Etche, ya ɗauki haramar zuwa gani da idonsa.

Kara karanta wannan

Da Dumi-dumi: Ministan Harkokin Waje Ya Rasu Ana Gab da Shiga Taron Ministoci

Dan siyasan ya bayyana cewa a hanyarsa ta zuwa ne yan daban suka bude masa wuta tare da magoya bayan da suke masa rakiya

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mai neman zama gwamna a Acoord Party ya nuna damuwarsa kan yadda abubuwa suka sauya a jihar Ribas. Ya ƙara da cewa jihar Ribas ta fara komawa abin tsoro.

Ya kara da bayanin cewa ya yi kokarin kiran wayar tarhon kwamishinan 'yan sanda na jihar Ribas, CP Okon Effiong Okon, amma bisa rashin sa'a lambarsa ta ƙi shiga.

Wannan harin na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan wasu abubuwan fashewa sun tashi a wurin gangami jam'iyyar a jihar Ribas. Lamarin ya jikkata wasu mambobin APC da dama.

Gwamna Wike Ya Yi Barazanar Soke Wurin da Atiku Zai Yi Kamfe a Ribas

A wani labarin kuma Gwamnan jihar Ribas, Nyeson Wike, ya yi barazanar fasa baiwa Atiku Abubakar babban filin yin kamfe a jihar

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin Da Yan Ta'adda Suka Bindige Kansila Har Lahira A Jihar Arewa

Gwamnatin jihar karkashin Wike ta amince da baiwa kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na PDP babban filin wasan Adokiye Amiesimaka don gudanar kamfe.

Wike yace an amincee musu amfani da filin ranar 11 ga watan Fabrairu amma ya ga wasu sun fara nuna iko tun yanzu, yace zai soke damar da aka basu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262