Sharbar Barci Kawai Tinubu Ya Yi Wurin Taron Yan Takarar Shugaban Kasa, Bai Ce Uffan Ba, Sowore

Sharbar Barci Kawai Tinubu Ya Yi Wurin Taron Yan Takarar Shugaban Kasa, Bai Ce Uffan Ba, Sowore

  • Kwamared Omoyele Sowore, dan takarar shugaban kasa na AAC ya caccaki Asiwaju Bola Tinubu na jam'iyyar All Progressives Congress, APC
  • Mawallafin na Sahara Reporters ya ce dan takarar shugaban kasar na APC barci kawai ya rika sharba yayin taron yan takarar shugaban kasa a ranar Juma'a
  • Kwamitin zaman lafiya na Najeriya ne ta kira yan takarar shugaban kasa da shugabannin jam'iyyun siyasa wurin taron

Omoyele Sowore, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar African Action Congress (AAC), ya zolayi Asiwaju Bola Tinubu dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulkin kasa.

Tinubu da Sowore na cikin wadanda suka halarci taron kwamitin zaman lafiya na kasa karkashin jagorancin Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya) da aka shirya a ranar Juma'a a Abuja.

Tinubu
Sharbar Barci Kawai Tinubu Ya Yi Wurin Taron Yan Takarar Shugaban Kasa, Bai Ce Uffan Ba, Sowore. Hoto: @YeleSowore
Asali: Twitter

A cewar Abdulsalami, an shirya taron ne don tabbatar da cewa yan takarar da jam'iyyunsu da magoya bayansu da sauran masu ruwa da tsaki sun yi harkokinsu cikin tsafta da bin doka musamman yayin kamfen gabanin zaben.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Atiku Abubakar Ya Dira Jihar Matashin Gwamnan G-5, Ya Shiga Matsala Tun a Filin Jirgi

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Awanni bayan kammala taron, Sowore ya rubuta a Twitter cewa Tinubu bai ce komai ba a wurin taron.

Barci Tinubu ya yi ta yi a wurin taro, shugaban APC na kasa ya yi jawabi a madadinsa, Sowore

Sowore ya rubuta:

"Yanzu muka dawo daga taron shugabannin jam'iyya da yan takarar shugaban kasa tare da kwamitin zaman lafiya na kasa a Abuja, dan takarar shugaban kasa na @OfficialAPCNg @officialABAT barci ya rika yi yayin taron, bai furta ko kalma daya ba. Shugaban jam'iyyarsa ya yi magana a madadinsa."

A baya, Daily Trust ta rahoto yadda Sowore ya kwashi yan kallo yayin da ya nuna kin yarda kan wurin zama, ya yi barazanar zai fita daga wurin wani taro.

Ya ce:

"Kamata ya yi a jera wurin zaman bisa yadda harrufa suke kamar ya faru a ICC yayin rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya kuma wannan ba adalci bane."

Kara karanta wannan

Dino Malaye Yace Ta Karewa Tinubu A Yankinsa Na Kudu Maso Yamma, Tunda Shugabannin Yankin Basa Yinsa

Janar Abdulsalami wanda ya bada tabbacin ya lura da hakan amma ya ce Sowore zai iya tafiya idan bai gamsu ba.

Zaben 2023: Ibo Sun karyata rahoton goyon bayan Bola Tinubu

Kungiyar yan kabilar Ibo da ke zaune a jihohin arewa 19 na Najeriya ta karyata cewa ta amince za ta goyi bayan Bola Tinubu, dan takarar jam'iyyar APC.

Cif Chi Ngozu da Austin Ifedinezi, shugaba da sakataren kungiyar ta ibo, sun ce labarin karya ne kawai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164