Bayan Gaza Samun Tikitin Shugaban Kasa, Kotun Koli Ta Ba Wa Akpabio Tikitin Sanata
- Kotun koli ta tabbatar da nasarar Godswill Obot Akpabio a matsayin dan takarar jam'iyyar APC na Akwa Ibom Northwest a zaben 2023
- Akpabio ya samu nasara a hukuncin da kotun ta bada ne a ranar Juma'a, 20 ga watan Janairu, bayan lokaci mai tsawo ana fafatawa
- Kafin hukuncin kotun, abokin hamyyarsa, Udom Ekpoudom ne ke kallubalantar tsohon gwamman a kotu
Abuja - Kotun koli ta tabbatar da zaben Sanata Godswill Akpabio a matsayin dan takarar sanata na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, na mazabar Akwa Ibom north-west a zaben 2023, rahoton The Cable.
Tsohon ministan dai yana cikin masu neman takarar tikitin shugabancin kasa na jam'iyyar, hakan yasa ba janye wa wani takarsa na sanata.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Karin Bayani: Hatsari Ya Ritsa Ya Tawagar Motoccin Shahararren Gwamnan Arewa A Hanyar Zuwa Kamfe, Yan Majalisa Sun Jikkata
Gabanin zaben fidda gwani na shugaban kasa na APC, Udom Ekpoudom, tsohon mataimakin sufeta janar na yan sanda, DIG, ya lashe zaben fidda gwani na Akwa Ibom north-west na yankin.
Ya yi karar APC da Akpabio a kotu, yana kallubalantar zaben Akpabio a matsayin dan takara, a maimakonsa.
Vanguard ta rahoto cewa kotun, a wani hukunci da alkalai biyar suka yi tarayya a kanta sun yarda da daukaka karar da Akpabio ya yi kan hukuncin kotun daukaka kara na soke takararsa.
Mai shari'a Ibrahim Saulawa a hukuncin da ya fitar a madadin sauran ya ce kotun daukaka karar ba ta da hurumin saka baki kan batun zaben dan takara na zabe, tana mai cewa lamari ne na cikin gida na jam'iyya.
Kotun kolin ta yarda da Akpabio kan batutuwa 10 da ya gabatar a gabanta don haka ta janye hukuncin da kotun daukaka kara da ke Abuja ta yanke a ranar 14 ga watan Nuwamba, 2022, wadda ta umurci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta amince da Ekpoudom a matsayin halastaccen dan takara.
Kotun daukaka kara ta kori Akpabio a matsayin dan takarar sanata na Akwa Ibom Northwest
A baya, kun ji cewa kotun daukaka kara wacce ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta kori Akpabio a matsayin dan takarar sanata na Akwa Ibom Northwest.
Mai shari'a Danlami Senchi, a madadin kwamitin alkalai uku ya ce Akpabio ya gaza gabatar da hujojji da kamar yadda kotun ta tanada.
Asali: Legit.ng