Peter Obi Ya Fita Daga Tseren Zama Shugaban Kasa a 2023, Omokri

Peter Obi Ya Fita Daga Tseren Zama Shugaban Kasa a 2023, Omokri

  • Reno Omokri, tsohon hadimin tsohon shugaban ƙasa yace tuni Obi ya fita da tseren zama shugaban kasa
  • A cewar Omokri, dan takara a jam'iyyar LP, Obi ba zai kai labari ba a watan Fabrairu saboda matsalar shiyyar kudu maso gabas
  • Tsohon gwamnan Anambra ya samu goyon bayan manyan mutane cikinsu harda tsohon shugaban kasa, Obasanjo

Tsohon hadimin tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan, ya yi ikirarin cewa tun tuni dan takarar shugaban kasa a inuwar Labour Party (LP) ya fita daga babban zaben 2023.

Reno Omokri ya yi musun cewa a hasashen da ya yi, shiyyar kudu maso gabas inda Peter Obi ke da karfi, ba zasu samu damar kaɗa kuri'a yadda ya kamata ba a watan Fabrairu.

Peter Obi da Omokri.
Peter Obi Ya Fita Daga Tseren Zama Shugaban Kasa a 2023, Omokri Hoto: thenation
Asali: UGC

Omokri ya bayyana cewa hangensa ya nuna cewa matsalar da ta dabaibaye shiyyar ne zata tsorata mutane su ƙi fitowa jefa kuri'a a ranar zabe, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: Mutane Za Su Yi Alfahari da Kasancewarsu Yan Najeriya Idan Na Gaje Buhari, Peter Obi

A kalamansa tsohon hadimin Jonathan watau Reno Omokri ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Za'a samu karancin fitowar jama'a a shiyyar kudu maso gabashin Najeriya saboda ayyukan ta'addancin kungiyoyin IPOB, ESN, da 'yan bindigan da ba'a sani ba."
"Wannan dalilin ya sa nake kyalkyata dariya idan na ji wasu mutane na cewa Peter Obi ne zai samu nasara a zabe."
"Shiyyoyin arewa maso yamma da kudu maso yammacin Najeriya ne zasu yanke abinda zai iya faruwa a zabe. Obi ba ya cikin masu tseren (zama shugaban kasa)."

Obi, tsohon gwamnan jihar Anambra, yana cikin manyan 'yan takara uku da ake ganin mai yuwuwa ɗayansu ne zai zama magajin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

Tsohon shugaban ƙasa, Chief Olusegun Obasanjo, ya bayyana goyon baya ga Peter Obi a sakon da ya aike wa matasan Najeriya na sabuwar shekara.

Kara karanta wannan

Kwankwaso Ya Tono Asalin Matsala, Ya Fadi Abu Ɗaya Tak Da Ya Kawo Yan Bindiga Arewacin Najeirya

Obasanjo yace duk cikin masu neman shugaban kasa babu waliyyi, amma idan aka dora su a sikelin kwarewa, gogewa, ilimi da sanin makamar aiki duk gara Obi.

Olubadan Ga Atiku: Ka Sasanta da Makinde da Sauran Gwamnonin G5

A wani labarin kuma Sarkin kasar Ibadan ya baiwa Atiku shawara kan abinda ya dace ya yi wa G5 gabanin babban zaben watan Fabarairu

Babbar basakaren Ibadanland, Oba Lekan Balogun, ya roki Atiku ya sulhunta da gwamna Makinde na Oyo da sauran gwamnonin G5.

Basaraken, wanda ya kira Atiku da abokinsa, ya nemi a Atiku ya duba matsayin sarakuna a Najeriya idan ya zama shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262