Bidiyon Yadda Aka Ceci Peter Obi Daga Dandazon Matasa a Wurin Kamfe Ya Bayyana

Bidiyon Yadda Aka Ceci Peter Obi Daga Dandazon Matasa a Wurin Kamfe Ya Bayyana

  • Matukin jirgin Helikwafta ya ceci dan takarar shugaban kasa a zaben 2023 karƙashin Labour Party, Peter Obi ranar Alhamis
  • Direban jirgin ya tseratar da tsohon gwamnan ne daga dandazon magoya baya, wadanda aka gaza shawo kansu a Enugu
  • Lamarin ya faru ne bayan Peter Obi ya kammala taro a jami'ar Najeriya dake Nsukka ya nufi Helikwaftansa zai tafi

Enugu - A ranar Alhamis, 12 ga watan Janairu, mai neman zama shugaban kasa a inuwar LP, Peter Obi, ya ziyarci jihar Enugu a ci gaba da yawon neman kuri'un jama'a gabanin zaben 2023.

Bayan kammala muhimman taruka da ziyarce-ziyarce a faɗin sassan jihar, wanda ya hada da halartar zauren al'umma a Jami'ar Nsukka, wasu dandazon mutane sun kusa murkushe dan takaran kafin shiga jirgi.

Peter Obi.
Bidiyon Yadda Aka Ceci Peter Obi Daga Dandazon Matasa a Wurin Kamfe Ya Bayyana Hoto: @Ozoadaz
Asali: Twitter

A wani Bidiyo da jaridar Legit.ng Hausa ta gani, ya nuna yadda tulin magoya baya suka mamaye wurin da aka aje Jirgin Helikwafta, wanda zai dauke shi su bar Enugu.

Kara karanta wannan

Zan Bayar Da Ilimi Kyauta Idan Na Zama Gwamnan Kano - Abba Gida-gida

Yayin da alamu suka nuna dandazon mutanen wadan ka iya yuwuwa akwai bara gurbi suka ci karfin dan takarar shugaban kasan, nan take matukin Helikwaftan ya ja hannun Peter Obi zuwa cikin jirgi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wasu daga cikin mutanen da suka nuna kauna ga dan takarar, an hangi suna yunkurin taɓa tsohon gwamnan jihar Anambra.

Martanin wasu yan Najeriya

Wasu yan Najeriya sun yi martani kan abinda ya faru da cewa Peter Obi ya cinye kasuwa watau ya saye soyayyar mutane daga fitowa neman takara.

Wani mau suna @Odoadaz a Tuwita ya ce:

"Peter Obi ya cinye kasuwa a jihar Enugu. Duba yadda suke jan shugaban kasar mu."

Wata mai amfani da @LyDimma ta ce Bidiyon ya taba mata zuciya:

"Abun tausayi, shi ne karo na karhe kamar a ce mahaifi ne zai yi tafiya amma ba ya kaunar ya rabu da 'ya'yansa."

Kara karanta wannan

'Dan Takarar Gwamna a 2023 Ya Yi Alƙawarin Kafa Gwamnati Bisa Koyi da Annabi Muhammad SAW

A wani labarin kuma Kwanaki 40 kafin zabe, manyan jam'iyyun siyasa sun rasa dubbannin mambobinsu da shugabanni

Jam'iyyar APC ta karbi tuban dubbannin mambobin PDP, NNPP da wasu jam'iyyu a jihar Neja yayin da kaddamar da kamfe a mazabar Sanatan arewacin Jihar. Daga cikin waɗan da suna sauya sheka har da tsoffin shugabannin PDP, maza da Mata da mambobin NNPP da wasu jam'iyyun siyasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262