Dalilin Da Yasa Jam'iyyar APC Zata Sake Samun Nasara A Zaben Jihar Kebbi

Dalilin Da Yasa Jam'iyyar APC Zata Sake Samun Nasara A Zaben Jihar Kebbi

  • Jam'iyyar APC, ta kaddamar da yakin neman zabenta a jihar Kebbi, inda gwamna Bagudu ke kammala wa'adinsa na biyu
  • Tsohon gwamnan jihar Usman Dakin Gari shine shugaban kwamitin yakin neman zaben gwamnan jihar
  • Jam'iyyar dai ta fara ne da karamar hukumar mulki ta Shanga, mai hedikwata a Shanga dan kaddamar da yakin neman zaben

Kebbi - Usman Dakin-Gari wanda yake a matsayin shugaban kwamitin yakin neman zaben jam'iyara APC a jihar Kebbi, yace jam'iyyar ce zata kara lashe zaben gwamna a jihar a zaben 2023. Rahotan PMNewsNigeria

Dakin-Gari na wannan kalamin ne lokacin da ake bude yakin neman zaben jam'iyyara na jihar a karamar hukumar mulki ta Shanga, babban birnin Shanga a jihar.

Ya ci gaba da cewa duba da yadda shugaba Muhammadu Buhari ya kawo aiyukan ci gaba a birni da karkara, to wannan ce manuniyar cewa lalle jama'ar Kebbi zasu zabi APC.

Kara karanta wannan

Sabon Matsala Ta Bullo A PDP Yayin Da Buhari Ta Yi Babban Zargi Kan Ayu

Daraktan ya kuma roki membobin jam'iyyar da su tabbatar da sun zabi jam'iyyar a kowanne mataki.

Dan Takara
Dalilin Da Yasa Jam'iyyar APC Zata Sake Samun Nasara A Zaben Jihar Kebbi Hoto: PMNews
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dakin-Gari bai gushe ba sai ya tabo batun noman shinkafa da Buhari ya samar da muhallin yinsa a jihar ta Kebbi, wanda kuma ya bunkasa aiyukan yi.

Dan takarar gwamna yayi alkawari

A nasa jawabin dan takarar gwamnan jihar Kebbi a tutar jami'iyyar APC, Dr Nasiru Idris yayi alkawarin maida hankali kan aiyukan da zasu raya kasa.

"Duba da yadda jam'iyyar APC, tai aiyukan raya kasa a lungu da sakon wannan jihar, idan kuka zabemu zamu tabbatar da mu samar da aiyukan da zasu bunkasa ci gaban ku"
"Ku zabi jam'iyyar mu ta APC dan ta bunkasa muku harkokin kasuwancinku, sabida in ba ita din ba wacce zaku zaba?

Kara karanta wannan

Saura Kwana 40 Zabe, Manyan Yan Takara Atiku da Kwankwaso Sun Yi Babban Rashi a Arewacin Najeriya

Kafin ya rufe jawabinsa sai da ya roki yan karamar hukumar da su maida hankali kan zabe kuma su tabbatar sunje sunkarbi katin zabensu.

A nasa bangaren kuwa shugaban jam'iyyar APC na jihar, ya nuna yadda jam'iyyar ta samar da aiyukan raya kasa a jihar

"yanzu ne lokacin da zaku ramawa kura aniyarta, ta hanyar zabar jam'iyyar mu"

Malami ya fasa takarar gwamna

Ministan shari'ar Nigeria Abubakar Malami SAN, ya fasa yin takarar gwamnan jihar Kebbi. Tunda fari dai an jiyo magoya bayan malamin na tabbatar da ministan zai yi takarar gwamna a jihar Kebbin.

To sai dai a lokacin da ministocin da zasuyi takara suke aje mukamansu, ba'a ga malamin ya ajiye ba, wanda hakan ke tabbatar da rashin takarar malamin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel