Yadda Manyan Takarar Shugaban kasa A Nigeria Ke Wawason Kuri'ar Arewa Maso Yamma

Yadda Manyan Takarar Shugaban kasa A Nigeria Ke Wawason Kuri'ar Arewa Maso Yamma

  • Manyan yan takarar shugaban kasa a Nigeria na wawason kuri'un yan arewa maso yamma duba da sune masu kuri'a mafi yawa a arewa
  • Babban dan takara daya ne dai ya fito daga yankin, kuma wanda bashi da tabbacin samun kuri;'ar yankin gaba daya.
  • Sauran yan takarar arewan sun fito ne daga yankin arewa maso gabas da kuma arewa maso tsakiya

Nigeria - Yan takarar shugaban kasa a Nigeria sun bazama tare da neman kuri'ar yan arewa maso yamma a Nigeria.

Yankin dai wanda shine a gaba wajen yawan wanda suke da rijista kada kuri'a a Nigeria, na fuskantar matsaltsalun rashin tsaro da kuma sauran fituntunu da suka yiwa yankin katutu.

Yan Takara
Yadda Manyan Takarar Shugaban kasa A Nigeria Ke Wawason Kuri'ar Arewa Maso Yamma Hoto: Vangauard
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Dantakarar Gwamna Na Jam'iyyar APC a Jihar Kano Yace Bai Yadda Akwai Rashawa a Gwamnati Ba

Nawa Ne yawan kuri'un yankin

Yankin na da yawan kuri'u kusan miliyan 22.2, wanda jihohin Kano. Kaduna, Sokoto, Katsina hadi da Kebbi da Jigawa suke

Shine yanki da ake da kuri'un da suke da yawan da idan takarar kadai ya sameshi zai iya kaiwa ga gaci.

Me yasa yan takara ke rububin yanki?

Iya jihar kano a yankin na bada kuri'u kusan Miliyan biyu da doriya. la'akari da zabuka uku da suka gabata, wato na 2011, 2015 da kuma 2019, duk yan takarar basa samun kuri'a sama da miliyan 20, to samun jihar kano ita kadai kan taimaka wajen yiwa abokin takara lahani.

Baya ga jihar Kano akwai johohin Kaduna, da Katsina da suma kan kawo irin wannan kuri'un, inda in an hada su zasu kai kusan miliyan 4.

In dai dan takarar ya samu kuri'a miliyan shida daga yankin arewa maso yamma a Nigeria, akwai hasashen zai iya kaiwa ga gaci.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Da Yiwuwan A Daina Taron Kamfe, Babban Dan takarar Shugaban Kasa Ya Kamu Da Sabuwar Nauyin Cutar Korona

Allah ya baka lafiya dattijo, Dino Malaye yayi ba'a ga Tinubu

Kakakin yakin neman Zaben jam'iyyar PDP, Dino Malaye ya tsakani dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, kan subul da bakan da yayi yayin yakin neman zabensa a Lagos.

Yayin da yake jawabi ga dimbin magoya bayansa a mahaifarsa dake Lagos, a ranar 26 ga watan Nuwanban shekarar 2023, ya bukace su da suje su karbi katin zabe.

A yayin da Tinubun ke kokarin fada musu hakan, yayi subul da baka yace APV, maimakon PVC.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida

Online view pixel