Babban Jigon APC Kuma Tsohon Kwamishina Ya Fice Daga Jam'iyyar
- Yayin da rage yan makonni babban zaben 2023, jam'iyyar APC mai mulki ta rasa babban jigo a jihar Ebonyi
- Dakta Paul Okorie, ya bayyana matakin da ya dauka na barin APC mai mulki a wata wasika da ya aike wa shugabannin jam'iyya
- Dan siyasan ya ce sun sha wahala matuka daga ba kowa suka gida APC ta zama wata tsiya a Ebonyi amma yanzun an mamaye su
Ebonyi - Wani babban jigon jam'iyyar APC reshen jihar Ebonyi, Dakta Paul Okorie, ya fice daga jam'iyyar a gundumarsa Mgbom ta 3 (Okposi) karamar hukumar Ohaozara.
Okorie, tsohon kwamishinan Ayyuka, Sufuri da gidaje ya bayyana fitarsa daga jam'iya mai mulki ne a wata wasika mai dauke da kwanan watan 3 ga watan Janairu, 2023.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Mista Okorie, ya zargi tsohuwar jam'iyarsa watau APC da rashin martaba 'ya'yanta musamman wadanda suka sadaukar da kansun wurin yi mata aiki.
Wani bangaren wasikar murabus daga mamban APC da ya rubuta, Okorie ya ce:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Lokacin da nake cikin jam'iyyar ina da kokari wurin sauke nauye-nauyen da ke kaina kuma na ba da gudummuwa gagara misali da karfina da dukiyata domin tabbatar da kafa APC tun daga tushe a Ebonyi."
"Tun da na shigo jam'iyyar a 2015 da sauran mambobi muka hada karfi da karfe muka gina APC. Garin gina jam'iyyar wasun mu sun rasa rayukansu wasu kuma sun rasa dukiyoyinsu."
"Wasu mambobin sun ji munanan raunuka daban-daban, wasu ma an kulle su a gidan Yari bisa zalunci amma jam'iyyar ta dauke idonta ba ta nuna kula da halin da suka tsinci kansu."
Jigon siyasan ya kara da bayanin cewa duk wannan wahalar da suka sha amma uwar jam'iyya ta kasa ta kyale sabbin shiga suka kwace jagorancin APC a Ebonyi aka bar tsoffin mambobi cikin halin lahaula.
Wata Sabuwa: Hadimin Gwamnan PDP Ya Yi Fatali da Atiku, Ya Fadi Dan Takarar Da Yake Goyon Baya a 2023
"Bisa wadan nan dalilai da na zayyano ne nake son sanar da ku sai wata rana ga dukkanin iyalan APC kuma ina wa jam'iyyar fatan Alheri."
Dan majalisa ya sauya sheka zuwa NNPP
A wani labarin kuma Jam'iyyar NNPP Mai Kayan Daɗi Ta Zama Babbar Jam'iyyar Adawa a Majalisar Dokokin Gombe
Bashir Yakubu Barau, mamba mai wakiltar mazabar Kantungo ta yamma a majalisar Gombe ya sauya sheka daga APC zuwa NNPP.
Hakan ya ba jam'iyya mai kayan alatu damar kasa-kasa da PDP, ta zama babbar jam'iyyar adawa a majalisar, tana da yan majalisu 4.
Asali: Legit.ng