Kotun Koli Ta Ayyana Umar Namadi Matsayin Sahihin Dan Takaran Gwamnan jihar Jigawa na APC

Kotun Koli Ta Ayyana Umar Namadi Matsayin Sahihin Dan Takaran Gwamnan jihar Jigawa na APC

  • Jigo a jam'iyyar APC, a jihar Jigawa ya shigar da kara gaban kotu yana kalubalantar zaben fidda gwanin jam'iyyar da akayi
  • Jigon yace akwai kurakurai masu tarin yawa da jam'iyyar da gwamnan jihar mai ci suka tafka yayin gudanar da zaben
  • Bayan faduwa a kotun kasa, jigon ya daukaka kara zuwa babban kotun tarayya dake zamanta a Abuja

Abuja - Kotun kolin Najeriya a ranar Juma'a ta tabbatar da sihhancin zaben fidda gwanin dan takarar gwamnan jihar Jigawa na APC inda, Umar Namadi, yayi nasara.

Kotu ta yi watsi da karar Hanarabul Farouk Adamu Aliyu, wanda ya bukaci kotu ta soke zaben.

Yayin yanke hukunci, Alkali Ibrahim Saulawa ya ce sam babu kamshin gaskiya cikin karar Farouk Adamu Aliyu.

Farouk
Kotu Ta Dage Sauraron Karar Da Dantakarar Gwamna Ya Shigar Yana Kalubalantar Nasarar Dan Takarar Gwamna Hoto: Premium Times
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Ana Daf da Zabe, Hukuncin Kotu ya Kuma Canzawa Jam’iyyar APC ‘Dan Takarar Sanata

Umar Namadi shine mataimakin gwamnan jihar Jigawa, wanda gwamnan ke kammala wa'adinsa na biyu.

Mai akai a shari'ar?

Alkalan dukka guda biyar sun yi ittifakin cewa ayi watsi da karar.

Umar Namadi, wanda ya samu wakilcin lauya, Prince Lateef Olasunkanmi Fagbemi, SAN, ya samu nasara a babban kotun tarayya da kotun daukaka kara a Kano.

Wanda hukunci na uku kuma ya samu nasara wanda ya kawo karshen muhawara kan sihhancin tikitin takarar gwamnan jihar na APC.

Muhawarar Kotu

Yayin da lauyan wanda ake kara ke kareshi a gaban kotu a ranar Larabar nan, Lateef Fagbemi, ya roki kotu ta kori karar da Farukun ya shigar sabida a kyale wanda yake karewa ya huta.

Fagbemi wanda yake da matsayin SAN, ya yace abinda Farouk din ya aikata baya cikin tsari da kuma ka'ida da ya kamata ace an saurareshi.

To sai dai a martanin lauyan wanda yake kara Onyechi Ikpeazu SAN, ya bukaci kotu da ta duba bukatar wanda yake karewa a gabanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida