Buhari Ya Gana da Dan Takarar Gwamnan Abiya Na APC, Ya Goya Masa Baya

Buhari Ya Gana da Dan Takarar Gwamnan Abiya Na APC, Ya Goya Masa Baya

  • Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya karbi bakuncin dan takarar gwamnan Abiya na APC, Ikechi Emenike, da matarsa
  • Shugaban ya kebe da mutanen biyu kafin daga bisani su ba shi kyautar zanen Hoton da aka dauka tun 2012
  • Buhari ya kuma daga hannun dan takaran yayin da ya ayyana cikakken goyon bayansa a zabe mai zuwa

Abuja - Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya karbi bakuncin dan takarar gwamnan jihar Abiya a inuwar jam'iyyar APC, Ikechi Emenike, ranar Alhamis 12 ga watan Janairu, 2023 a Aso Villa.

Jaridar Punch ta rahoto cewa shugaban kasa ya gana da ɗan takarar tare da mai dakinsa kuma Jakadar Najeriya a kasar Amurka, Uzoma Emenike.

Shugaba Buhari da dan takarar APC a Abiya.
Buhari Ya Gana da Dan Takarar Gwamnan Abiya Na APC, Ya Goya Masa Baya Hoto: Buhari Sallau/facebook
Asali: Facebook

Mista Emenike tare da matarsa, wanda aka gano sun isa fadar shugaban kasa da misalin karfe 3:15 na rana, sun gana da Shugaba Buhari a kebance.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Dan Takarar Gwamna Ya Riga Mu Gidan Gaskiya, Jam'iyya Ta Maye Gurbinsa

Bayan wannan ganawa ne, ma'auratan suka gabatarwa shugaban kasan kyautar zanen Hoton wanda aka dauka tare da Buhari tun a shekarar 2012.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Buhari ya goya wa dan takarar baya

Bayan haka, shugaban kasan ya kuma ayyana cikakken goyon bayansa ga Mista Emenike ya zama gwamnan jihar Abiya a babban zaben gwamnonin da ke tafe a watan Maris.

Buhari ya daga hannun dan takarar domin tabbatar wa 'yan Najeriya musamman mutanen Abiya cewa yana tare da burin jigon APC na zama gwamna.

Shugaba Buhari.
Buhari Ya Gana da Dan Takarar Gwamnan Abiya Na APC, Ya Goya Masa Baya Hoto: Buhari Sallau/facebook
Asali: Facebook

PDP ta yi rashin nasara a Kotu

Idan baku manta ba, Kotu mai zama a Owerri, babban birnin jihar Imo ta yi fatali da karar da jam'iyyar PDP ta shigar gabanta, ta nemi a dakatar da Emenike daga neman kujerar gwamna a inuwar APC.

A karar mai lamba CA/OW/473/2022 da PDP ta shigar tana kalubalantar INEC da APC, Kotun karkashin mai shari'a Rita Pemu, ta yanke cewa Emenike ne sahihin dan takarar APC.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP: Bana goyon bayan Atiku, ba kuma zan tursasawa 'yan jiha ta su bi ra'ayi na ba

Vanguard ta tattaro cewa PDP ta nemi a rushe zaben fidda gwanin APC ne bisa hujjar cewa jam'iyar ta saba wa dokokin zabe.

A wani labarin kuma Kungiyoyin Kwadugo Sun Ayyana Goyon Bayansu Ga Bola Tinubu da Gwamnan APC

Kungiyar kwadugo ta ayyana cikakken goyon bayanta ga dan takarar shugaban kasa, Alhaji Bola Tinubu yayin da ake gab da zaben 2023. Tinubu na daya daga cikin manyan yan takara na sahun gaba da ake ganin zasu iya darewa kujera lamba daya Najeriya bayan Buhari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262