Ba Ni da Ko Bulo a Ketare, Ina Bautawa Ubangiji da ‘Yan Najeriya, Buhari
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa ba shi da ko bulo daya a kasar ketare don haka babu wanda zai bata masa suna kan hakan
- Ya bayyana yadda ya shawo kan matsalar Boko Haram wacce ya gada daga mulkin da ya gabata kuma hakan yasa yace ya cika alkawarin da ya dauka
- Ya magantu kan matsalar rashawa inda yace mulkin yanzu ba na soja bane, shiyasa yaki da rashawa ke da matukar wahala
Damaturu, Yobe - Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace babu wani zai bata masa suna kan dukiya ko kudin haram da ya azurta kansa da shi yayin da ya ke ofis inda yace bashi ko bulo daya a ketare.
A yayin jawabi a filin taro na Banquet daren Litinin a Damaturu babban birnin jihar Yobe, shugaban kasan ya jaddada cewa ya sha alwashin bautawa Najeriya da Ubangiji har zuwa kwanakinsa na karshe a ofishinsa da gaba da hakan, Channels TV ta rahoto.
Ya shawarci ‘yan Najeriya da su kasance masu kishin kasa inda:
“kamar yadda nace sama da shekaru 30 da suka wuce, ba mu da kasa da ta wuce Najeriya, dole ne mu zauna cikinta tare ceto ta tare.”
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya kara da cewa manyan matsalolin tsaron da mulkinsa ya gada daga mulkin baya shi ne ya zama ta’addanci amma ya bayyana jin dadinsa kan yadda komai ke dawowa daidai a jihohin da lamarin ya shafa a yankunan arewa maso gabashin Najeriya.
A don haka ya bayyana cewa ya cika alkawurran da yayi wa ‘yan Najeriya a rantsuwarsa da yayi ta ranar 29 ga Mayun 2015 a jawabinsa da yayin na shawo kan ta’addancin Boko Haram tare da kawo daidaito a Najeriya, jaridar Daily Trust ta rahoto.
“A arewa maso gabas, Ubangiji ya taimake mu mun magance Boko Haram, tattalin arziki ya dawo kuma wasu jama’ar na tambayata nasarar da na samu kan alkawarin yaki da rashawa.
Uba Ya Fashe Da Kuka Yayin da Karamar Diyarsa Ta Yi Alkawarin Siya Masa Mota, Bidiyon Ya Haddasa Cece-Kuce
“Toh a karkashin wannan tsarin yaki da rashawa bashi da sauki. A yayin da nake soja kuma nake shugaban kasa, na garkame wasu saboda kundin tsarin mulki yace dole a bayyana kadara kuma duk wanda ya kasa na rufe shi.
“A karshe ni ma garkame ni aka yi. Toh idan ka na son bautawa kasar nan, dole ka shiryawa mafi muni. Amma abu daya da zan godewa Allah a kai shi ne, babu wanda ya isa ya bata min suna.
“Bani da ko bulo daya a ketaren Najeriya kuma ina da niyyar zama a Najeriya idan nayi murabus daga aikin Gwamnatin.”
Buhari ya kaddamar da kamfen din Tinubu da Binani a Adamawa
A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dira har jihar Adamawa inda ya kaddamar da yakin gangamin neman zaben Bola Ahmed Tinubu da Aishatu Binani a jihar.
Asali: Legit.ng