Zaben 2023: Tinubu Ya Bincika Tarihin Peter Obi, Ya Nada Masa Sabon Suna
- A ranar Asabar, 7 ga watan Janairun 2023, an nada wa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour, Peter Obi, sabon suna
- Asiwaju Ahmed Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC ne ya nada wa Obi sabuwar sunan a jihar Ondo
- A cewar Tinubu, mutanen jihar Anambra sun sha wahala a yayin da Obi ya ke alfahari da kansa cewa shi ya tare kudi ya adana a baitil mali
Jihar Ondo - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana takwararsa na jam'iyyar Labour a matsayin 'Mr Stingy' wato marowacci ko mai mako, rahoton The Cable.
A yayin kamfen dinsa na shugaban kasa da ya tafi yi a Ondo a ranar Asabar, 7 ga watan Janairu, ya yi ikirarin cewa makon Obi ta yi yawa don haka bai dace a bashi mulkin Najeriya ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewarsa, a lokacin da Obi ke gwamna, mutanen jihar Anambra suna fama da yunwa yayin da shi Obi yana can yana adana kudi.
Tsohon gwamnan na jihar Legas, cikin sanarwar da Legit.ng ta samu, ya yi ikirarin cewa abin da Obi kawai ya yi shine alfahari cewa ya adana kudi yayin da akwai yunwa a jihar.
Don wannan dalilin, Tinubu, yayin da ya ke magana game da Obi ya ce shi gwamna ne mara tausayi wanda zai boye kudi yayin da mutane na cikin yunwa, makarantu, hanyoyi, asibitoci kuma suna lalacewa, yana mai cewa yan birni da yan karkara duk ba su bunkasa ba a mulkinsa.
Tinubu ya kara da cewa:
"A karshe, ya ki ceton mutane domin ya gwammace ta adana kudi.
"Kuma yana ikirarin yana jam'iyyar ma'aikata. Za ku wahala sosai idan kuna tunanin zai yi abin da ya fi wanda ya yi a Anambra a kasar."
Da ya ke bayyana manyan banbanci tsakaninsa da Obi, Tinubu ya ce duk da cewa Legas ba ta da fili sosai yayin da Anambra na da yalwa, mafi yawancin mutanen Anambra su kan taho Legas don neman arziki saboda tsarin da ya bari a Legas.
Don haka, ya yi kira ga yan Najeriya kada su mika makomarsu a hannun marowacin shugaba, amma, su bashi goyon bayan, ya kira kansa a matsayin 'Mr Progressive Governance' wato mai gwamnatin cigaba.
Asali: Legit.ng