Gwamnonin PDP Biyu Sun Ziyarci Okowa, Sun Nanata Bukatar Hada Kai da G5
- Gwamnan Bayelsa, Duoye Diri, da takwaransa na jahar Edo, Godwim Obaseki sun ziyarci dan uwansu na Delta, Ifeanyi Okowa
- Yayin ziyarar gwamnonin sun nuna bukatar sake zama domin shawo kan gwamnonin G5 na tsagin Wike
- Gwamnan Edo yace sun kai wa Okowa ziyara ne da nufin kara dankon zumunci da fatan Alheri
Delta - Gwamnan jihar Bayelsa, Duoye Diri, yace hadin kai a jam'iyar PDP ne abinda zasu sanya a gaba a lokacin da babban zaben 2023 ke kara matsowa.
The Cable ta ruwaito cewa Gwamna Diri ya faɗi haka ne yayin da yake zantawa da manema labarai bayan shi da Gwamnan Edo sun kai ziyara ga gwamna Ifeanyi Okowa a jihar Delta.
Diri ya ce jam'iyyar PDP na fatan sake zama da tawagar G5 domin rarrashinsu su marawa wa jam'iya baya kuma su tallata dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar.
"Muna son haɗa kan PDP kuma a duk lokacin da muka zauna, muna maida hankali mu tattauna kan hadin kai, har yanzu bamu cire ran shawo kan 'yan uwanmu ba."
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Muna kira ga 'yan uwanmu gwamnoni su dawo ba da gudummuwa a jam'iyarsu kuma su taimaka wurin dunkulewa wuri daya. Muna son yan uwanmu gwamnonin su dawo don mu ci gaba da zumunci."
"Muna son rika kai masu ziyara kamar yadda yanzu muka zo wurin Okowa, wanda da ikon Allah zai zama mataimakin shugaban kasa a Najeriya."
- Duoye Diri.
Da yake jawabi a wurin ganawarsu, gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo yace sun zo ne su taya Okowa murna tare fatan Alheri a zabe mai zuwa.
"Mun shigo sabuwar shekara, muna zuwa wurin yan uwanmu tare da masu fatan Alheri da addu'a tagari. Yau gamu wurin Okowa, dan takarar mataimakin shugaban kasa."
"Muna masa fatan Alheri kuma da izinin Allah zai zama mataimkin shugaban kasa na gaba. Muna Addu'a Allah ya sa mafarkin mu ya zama gaskiya a 2023."
- Godwin Obaseki.
SDP Ta sanar da kwamitin PCC
A wani labarin kuma Khadijat, Matashiyar Da Ta Nemi Takarar Shugaban Kasa Ta Samu Babban Mukami a PCC
SDP ta nada Khadijah Okunnu-Lamidi a matsayin mataimakiyar daraktan janar na kwamitin kamfen shugaban ƙasa 2023.
Khadijah ta nemi takarar shugaban kasa amma ta sha kaye a zaben fidda gwani hannun Adewole Adebayo.
Asali: Legit.ng