Tsohon Gwamnan APC Ya Bayyana Dan Takarar da Allah Yace Zai Zama Shugaban Kasa a 2023
- Atiku Abubakar da Peter Obi sun yi batan dabo yayin da tsohon gwamnan Osun ya bayyana wani sirri game da zaben 2023
- Oyetola a ranar Litinin ya bayyana cewa Allah ya gaya masa Bola Ahmed Tinubu ne zai zama shugaban kasa na gaba
- Ya kuma sha alwashin cewa zai sake koma wa gadon mulkin jihar Osun inda ya ce ya tafi ne ya dan sarara ya samu hutu
Osun - Tsohon gwamnan jihar Osun da ya sauka a kwanakin baya, Adegboyega Oyetola, yace an masa wahayin cewa dan takarar shugaban kasa a inuwar APC, Bola Tinubu, ne zai lashe zaben 2023.
Mista Oyetola ya kara da cewa Allah ya faɗa masa cewa zai sake komawa kan madafun iko na mulkin jihar Osun.
Ya kuma yi kira ga mambobin APC da su tashi tsaye haikan su yi aiki tukuru domin ganin dukkanin 'yan takarar APC sun kai ga nasara a zabe mai zuwa, kamar yadda Punch ta rahoto.
Oyetola ya bayyana abinda Allah ya faɗa masa
Da yake jawabi a wurin taron Addu'o'i da manyan APC suka shirya a Osogbo ranar Litinin, tsohon gwamnan yace ya jagoranci Osun yadda ya kamata lokacin yana kan mulki.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya kara wa mambobin APC karsashi da cewa su ci gaba da kokari yadda ake tsammani kuma su kauce wa duk wani abu da zai iya dauke masu hankali.
Ya kuma roki su karbo katunan zabensu sannan su tabbata sun kaɗa wa Bola Tinubu kuri'unsu a zaben shugaban kasan dake tafe.
Oyetola ya ce:
"Allah ya faɗa mun zai mana abu biyu a wannan shekarar 2023. Zamu dawo da hakkin mu na kujerar gwamna kuma Asiwaju Bola Tinubu, zai zama shugaban kasa a Najeriya."
"Na san kun tsorata da abunda ya auku amma Allah yana da tanadi a gare mu. Kowa na da kalar kalubalensa, na tafi hutu ne. Kun ga yadda na kara kyau yanzu."
"Na yi wa Osun aiki bil hakki da gaskiya tsawon shekaru hudu ba tare da hutu ba, Allah na sane ya tsara mun haka domin na samu hutu."
Hadimin Atiku Ya Nemi Gwamna Wike Ya Baiwa Mutane Uku Hakuri
A wani labarin kuma Rigingimun jam'iyar PDP na kara tsananta bayan Wike ya sake fallasa wata manaƙisar Atiku tun a 2023
Sai lamarin bai yi wa makusantan Atiku dadi ba, inda aka ji Phrank Shaibu ya fito yana neman Wike ya baiwa mutane uku hakuri tun da wuri..
Wike da sauran mambobin tawagarsa na G-5 sun kafe kan bakatarsu wacce har yanzun babu alamun za'a iya biya masu ita a PDP.
Asali: Legit.ng