Mamman Daura Ya Fadi Dalili 1 da Ya Hana Buhari Zama Shugaban Kasa Tun 2003

Mamman Daura Ya Fadi Dalili 1 da Ya Hana Buhari Zama Shugaban Kasa Tun 2003

  • Malam Mamman Daura ya na ganin murdiya ce ta hana Muhammadu Buhari nasara a 2003, 2007 da 2011
  • Dattijon ya ce rashin sa’ar da suka samu a ANPP da CPC ya tilasta masu yi wa jam’iyyar PDP taron dangi
  • Saboda irin magudin zaben da aka rika yi, Daura ya ce Buhari ya hakura da takara, har ya yi wa mulki kuka

Abuja - Mamman Daura wanda ‘danuwa ne kuma na hannun daman Muhammadu Buhari ya na ganin ba ayi adalci a zabukan da aka shirya a baya ba.

Premium Times a ranar Litinin, 2 ga watan Junairu 2022, ta rahoto Malam Mamman Daura yana zargin jam’iyyar PDP ta yi magudi a 2003, 2007 da 2011.

Daura yake cewa mummunan murdiyan da aka buga a zabukan kasar da kuma rashin yarda da tsarin zaben ya jawo Muhammadu Buhari ya sare.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Zauna da Fastoci a Aso Villa, Ya Fada Masu Gaskiyar Batun Ɗaga Zabe

Yayin da yake yawon yakin neman zaben 2011, Muhammadu Buhari ya cire rai da samun mulki, a dalilin wannan aka ga yana kuka a bainar jama'a.

Essential Muhammadu Buhari

Legit.ng ta fahimci an tsakuro jawabin dattijon ne a wani shiri mai suna “Essential Muhammadu Buhari” da aka fitar a kan tarihi da rayuwar shugaban kasar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An yi hira da Daura game da takarar da ‘danuwansa ya yi wajen neman zama shugaban kasar Najeriya a zabukan da aka yi a shekarun 2003, 2007 da 2011.

Takarar Shugaban Kasa
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari wajen kamfe Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Takara 3 a jere babu nasara

A takaran da Buhari ya yi a wadannan lokuta a APP, ANPP da CPC, ya sha kashi a hannun Olusegun Obasanjo, Umaru Yar’Adua da Dr. Goodluck Jonathan.

Da ya je wajen kamfe a 2010, Buhari ya fadawa Duniya cewa ba zai sake tsayawa neman mulki ba, ya na hawaye yake fadawa jama’a ya yi takararsa na karshe.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Bayyana Ainihin Manufar Ƙirƙirar Ƙungiyar Boko Haram

A cewar Malam Daura, da ya karbi sakamakon zaben shugaban kasa na wasu jihohi a zaben 2007, ya fahimci babu shakka an tafkawa jam’iyyar ANPP magudi.

"Lauyan ya ba ni sakamakon zaben jihar Imo. Da na duba sakamakon da kyau, sai na ga PDP, Yar’adua ya samu kuri’u 25, 000, Buhari ya na da 5, 000.
A duka sakamakon, za a ga an daidaita adadin kuri’un. Har wanda ya yi nasara, Yar’adua ya ce zaben da matsala."

- Mamman Daura

Linda Ikeji ta rahoto Daura yana cewa ganin murdiyan da aka yi sau uku, Buhari ya hada-kai da sauran jam’iyyu a 2013, a karshe ya dare kan mulki a 2015.

Dalilin tsaida Tinubu a APC - Wammako

Dazu aka ji labari Aliyu Magatakarda Wamakko ya yi zama da Hausa, Yarbawa, Ibo, da sauran kabilu, ya yi masa bayanin hikimar tsaida Bola Tinubu a APC.

A wani taro da aka yi a gidansa da ke garin Sokoto, kabilu dabam-dabam sun yi wa Sanata Aliyu Wamakko alkawarin goyon bayan jam'iyyarsa ta APC a 2023.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Ce Ya Cika Alkawuran da Ya Dauka, Tinubu Ya Ce ba Haka Abin Yake ba

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng