Magana Ta Kare, Obasanjo Ya Fadi Dan Takarar Da Yake Goyon Baya a 2023
- Chief Olusegun Obasanjo ya ayyana goyon bayansa ga dan takarar shugaban ƙasa a inuwar LP, Peter Obi a zabe mai zuwa
- Tsohon shugaban kasan yace duk cikin masu neman takara babu waliyyi amma Obi ya zarce sauran cancanta
- Wannan nq zuwa ne a daidai lokacin da jam'iyyar PDP ke fama da rigingimun ciki gida musamman kan batun G-5
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya fito fili ya ayyana goyon baya ga dan takarar shugaban ƙasa a inuwar Labour Party, Peter Obi, yayin da ya rage kasa da watanni biyu zaben 2023.
Dailytrust tace Obasanjo ya bayyana wa 'yan Najeriya zabinsa ne a sakon murnar shiga sabuwar shekara mai taken, "Rokon da nake wa 'yan Najeriya musamman matasa."
Tsohon shugaban yace duk cikin masu hangen zama shugaban kasa a 2023 babu waliyyi, amma idan idan aka dora su a Sikelin ilimi, gogewa da abinda zasu iya yi, Peter Obi ya masu fintinkau.
"Babu waliyyi a cikin masu neman takara amma idan aka diba halayensu, tarihinsu, fahimtar da suke da ita, ilimi, gogewa da abinda zasu iya jurewa da bukatar da ake da ita duba da yadda kasa ke ciki."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Kuma a duba kwarewarsu kan aiki ni a karan kaina na zabi Peter Obi, domin ya masu zarra. Sauran mutane irin mu suna da gudummuwar da zasu bayar a haɗa karfi a ceto Najeriya."
"Wani abu mai muhimmanci game da Obi shi ne ya zama tamakar allura da zaren dinke arewa da kudu kuma ba zai taba faɗuwa ba."
- Obasanjo.
Obasanjo ya kara da cewa Obi ya zakulo matashi mai jini a jika a matsayin abokin takararsa kuma yana da wadan da zasu ja hankalinsa idan ya kauce hanya.
A rahoton Punch, Obasanjo ya kara da cewa:
"A wani bangaren kuma yana da masu jan kunnensa idan bukatar hakan ta taso, bugu da kari kuma yana tare da abokin takara matashi, wanda ke da tarihin cin nasara a gwamnatance da gefen zaman ƙashin kai."
Hadimin Atiku Ya Nemi Gwamna Wike Ya Baiwa Mutane Uku Hakuri Kan Kalamansa
A wani labarin kuma Wani hadimin Atiku Abuabakar ya bukaci Wike ya baiwa, Obasanjo, dan takarar shugaban kasa na PDP da iyalan tsohon minista hakuri
Alaka na kara tsami tsakanin Atiku Abubakar da Wike, hadimin dan takarar shugaban kasa na PDP ya dirararwa gwamna Ribas kan asirin da ya tono. Wike dai yace a 2003, sai da Obasanjo ya duka kan guiwa ya roki Atiku ya bari ya nemi tazarce amma duk da haka sai da ya gindaya masa sharudda.
Asali: Legit.ng