Atiku Yayi Wani Abin Ban Mamaki, Ya Sace Zuciyar Ƴan Najeriya da Dama

Atiku Yayi Wani Abin Ban Mamaki, Ya Sace Zuciyar Ƴan Najeriya da Dama

  • Dan takarar shugaban kasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar, ya nuna halin girma duk da rigingimun dake tsakaninsa da G-5
  • Tsohon mataimakin shugaban kasa ya taya gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo murnar zagayowar ranar haihuwarsa
  • Mutane sun yi martanu da cewa duk da sabanin dake tsakaninsu, Atiku ya aika masa da sakon kalamai masu daɗi

Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, yayi wani abin ban mamaki wanda ya sanya mutane da dama a kafafen sada zumunta suka yaba masa.

Atiku Abubakar ya samu wannan yabon ne bayan ya taya gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, murnar zagayowar ranar haihuwar sa a shafinsa na sada zumunta.

Gwamna Makinde da Atiku.
Atiku Yayi Wani Abin Ban Mamaki, Ya Sace Zuciyar Ƴan Najeriya da Dama Hoto: Pmnewsnigeria
Asali: UGC

Gwamna Seyi Makinde yana ɗaya daga cikin gwamnoni biyar na PDP waɗanda suka ce lallai idan har Atiku yana son ya samu goyon bayan su sai shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Iyorchia Ayu, yayi murabus daga kan muƙamin sa.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Sake Shiga Tasku, Gwamna Arewa Ya Ayyana Ɗan Takarar Da Zai Marawa Baya a 2023

Sai dai, duk da saɓanin dake a tsakanin su, Atiku ya taya Makinde murnar zagoyar ranar haihuwar sa a kafafen sada zumunta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Atiku ya wallafa a shafinsa na Tuwita cewa:

"Ina taya ka murnar zagayowar rinar haihuwar ka da bikin kirismeti @seyimakinde."
"A madadin iyalai na da yan tawaga ta, ina maka fatan ƙara shekaru masu yawa cikin ƙoshin lafiya sannan da cigaba da yiwa mutanen jihar Oyo da Najeriya ayyukan arziƙi."

Yadda sakon ya yi wa mutane daɗi

Wannan rubutun ya sanya mutane da dama sun yaba wa Atiku a kafafen sada zumunta inda suka bayyana shi a matsayin gogaggen ɗan siyasa.

Wani mai suna Yahuza Hamza ya rubuta:

"Duk da irin abubuwan da gwamnonin G5 suka yi kuma suke cigaba da yi domin ganin sun ɓata maka rai da jam'iyyar mu, amma ka taya shi murnar zagayowar ranar haihuwar sa, lallai kai shugaba ne."

Kara karanta wannan

Babban Jigon Siyasa Ya Bayyana Abinda Ka Iya Faruwa da APC, Tinubu a Zaben 2023

"Sannan da yardar ubangiji kai za'a naɗa shugaban ƙasa na gaba idan 2023 ta zo."

Wani mai sharhi ya rubuta:

Lissafi na kan nasarar ka yana da tabbacin kaso 85. Nasara taka ce. Addu'a ta itace ka zama shugaban ƙasa ga dukkan 'yan Najeriya ba tare da la'akari da ƙabila, addini ko ɓangare ba."
"Na ga shirin da kake da shi kan tsaro, hakan shine abinda ƙasar mu ke buƙata."

Wani mai suna Jade ya rubuta:

"Kai shugaba ne! Nuna musu ƙauna sai kayi galaba akan su, mu gama da wannan ranka ya daɗe. Na ga irin muhimmin tasirin da hakan zai yi, bayan da cewa ko tantama babu zaka lashe zaɓen nan ko da kuwa yau za a yi shi."

Tsohon Sanatan PDP ya mutu

A wani labarin kuma Babban Dan Kashenin Atiku Kuma Tsohon Sanatan PDP Ya Rasu a Asibitin Abuja

Tsohon Sanatan jam'iyyar PDP a mazaɓar Bayelsa ta gabas, Inatimi Spiff, ya rigamu gidan gaskiya a wani asibitin babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Bayan Raba Gari da Atiku, Gwamnonin G5 Sun Fara Kulla-Kullar Wanda Zasu Mara Wa Baya a 2023

Jam'iyyar PDP ce ta sanar da mutuwar jigon siyasan wanda ya yi fama da rashin lafiya ta ɗan lokaci kafin rai ya yi halinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262