2023: Ku Dangwalawa Peter Obu Kuri'unku Zai Iya Ceto Najeriya, Gwamna Ortom

2023: Ku Dangwalawa Peter Obu Kuri'unku Zai Iya Ceto Najeriya, Gwamna Ortom

  • Gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, ya nuna goyon bayansa ga ɗan takarar shugaban kasa a inuwar LP, Peter Obi
  • Mista Obi, tsohon gwamnan jihar Anambra ya ziyarci wurin 'yan gudun hijira inda ya yi shagalin kirsimeti tare da su
  • Gwamna Ortom na ɗaya daga cikin gwamnonin G5 da suka raba gari da Atiku Abubakar

Benue - Gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, ya fito fili ya ayyana cikakken goyon bayansa ga ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar Labour Party, Peter Obi, gabanin babban zaɓen 2023.

Jaridar PM News ta tattro cewa gwamna Ortom, mamban tawagar gaskiya G-5, ya bayyana haka ne bayan ya karbi bakuncin Peter Obi a gidan gwamnatinsa ranar Lahadi.

Peter Obi da Ortom.
2023: Ku Dangwalawa Peter Obu Kuri'unku Zai Iya Ceto Najeriya, Gwamna Ortom Hoto: Peter Obi
Asali: Facebook

Gwamnan ya yaba wa ɗan takarar shugaban kasan bisa karamci da nuna kulawa na ziyartar 'yan gudun hijira a jihar Benuwai tare da shagalin murnar zagayowar kirskmeti tare da su.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP Ya Faɗi Shirin da Tawagar G-5 Ke Kulla wa Game da Babban Zaben 2027

Haka zalika ya bayyana Obi, tsohon gwamnan jihar Anambra da mutumin da ya dace, wanda zai iya warware matsalolin da suka kewaye Najeriya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Gwamna Ortom ya ce:

"Masu neman zama shugaban kasa da dama sun zo nan kuma babu ɗaya da ya ce bari ya je sansanin 'yan gudun hijira ya ga yadda rayuwarsu take. Amma kai ka zaɓi murnar kirsimeti tare da su maimakon cikin iyalanka."
"A matsayin Kirista ina rokon Allah ya maka albarka ya taimakeka, ina addu'a Allah ya taimaki burinka na zama shugaban kasa, saboda na ga kwarewa, imani da fata nagari a tattare da kai."
"Kuma na hangi mutum wanda zai kawo adalci da daidaito abinda na ke ta fafutuka tunda na zama gwamna a 2015. Da bana cikin PDP da kafarka kafata zamu rika yawo neman kuri'un yan Najeriya."

Kara karanta wannan

Bayan Raba Gari da Atiku, Gwamnonin G5 Sun Fara Kulla-Kullar Wanda Zasu Mara Wa Baya a 2023

Daga nan gwamna Orton ya yi kira ga 'yan Najeriya da su zaɓi Peter Obi domin shi ne ɗan takarar da zai iya taimakonsu da Najeriya baki ɗaya.

"Saboda ni mamban PDP ne ina mai faɗawa 'yan Najeriya cewa wannan mutumin (Obi) zai iya tsamo Najeriya daga kalubalen da take ciki."

Ku Mun Biyayya da PDP Ko Na Kori Mutum Daga Aiki, Gwamnan Arewa Ya Gargadi Hadimansa

A wani labarin kuma Gwamnan Bauchi ya gargaɗi kwamishinoni da hadimansa su masa biyayya ko su rasa aikinsu

Gwanna Bala Muhammed da ake kira da Kauran Bauchi ya yi barazanar korar duk wani mai rike da kujerar siyasa da aka gano ba shi da ɗa'a.

Gwamnan ya rantsar da sabbin kwamishinoni biyu da Kantomomi a kananan hukumoni 20 na jihar Bauchi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262