Wani Babban Jigon APC Ya Bayyana Yadda Sakamakon Zaben 2023 Zai Wa Tinubu

Wani Babban Jigon APC Ya Bayyana Yadda Sakamakon Zaben 2023 Zai Wa Tinubu

  • Wani jigon jam'iyyar APC kuma tsohon ɗan takara a jihar Ekiti ya yi hasashen nasara ga APC da Bola Tinubu
  • Tsohon gwamnan Legas kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar APC na da karfi a shiyyar kudu maso yamma
  • Manyan yan takara irinsu Atiku Abubakar na PDP, Peter Obi na LP da Kwankwaso na NNPP ne zasu fafata da Tinubu

Ekiti - Wani babban jigon jam'iyyar APC a jihar Ekiti, Ayodeji Adarabierin, ya yi hasashen cewa ɗan takarar shugaban kasa a inuwar jam'iyya mai mulki, Bola Ahmed Tinubu ne zai lashe zaɓen 2023.

The Nation ta rahoto Adarabierin ya ayyana jihar Ekiti da shiyyar kudu maso yammacin Najeriya a matsayin ginshiƙin nasarar APC da kuma Asiwaju Tinubu.

Bola Ahmed Tinubu.
Wani Babban Jigon APC Ya Bayyana Yadda Sakamakon Zaben 2023 Zai Wa Tinubu Hoto: Bola Tinubu
Asali: Getty Images

Jigon ya kuma ƙara da cewa 'yan takarar kujerun majalisar dokokin jihar Ekiti da na majalisun tarayya na APC zasu samu nasara a babban zaɓe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Musayar Yawu Ta Ɗau Zafi, Wike Ya Maida Zazzafan Martani Ga Tsohon Shugaban PDP

Mista Adarabierin, tsohon ɗan takarar mamban majalisar dokokin jiha a mazaɓar Ado ta I, ya yi wannan hasashen ne a Ado-Ekiti, babban birnin jihar yayin wani shagali da ya shirya wa yan mazabarsa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yace zai zauna ya saurari mutanen mazaɓarsa da waɗanda ba su da alfarmar ganinsa, "Amma an shirya wannan ne don kara dankon zumunci da yan uwa da iyalansa na siyasa waɗanda suka kafe a bayansa a zaben fidda gwani."

Shin wa zai samu nasara a zaben 2023?

Da yake tsokaci kan yuwuwa da damar jam'iyar APC a zaɓe mai zuwa, Mista Adarabierin ya ce:

"Muna da manyan ayyuka a gaban mu amma hakan ba yana nufin ba zamu kai labari bane, babu wata nasara dake zuwa a kwance."
"Ina rokon abokanmu, iyaye da jagorori a siyasa da su yi aiki tukuru don cimma nasara a zabe mai zuwa."

Kara karanta wannan

2023: Sarkin Katsina Ya Faɗi Wanda Zai Iya Zama Shugaban Kasa Yayin da Ya Karbi Bakuncin Atiku

Jigon, wanda ya yi hasashen Tinubu zai lashe kuri'un Ekiti, ya ƙara da cewa:

"Wannan jihar da ma sauran jihohin kudu maso yamma bango ne ga APC da Asiwaju, mun gode Allah saboda muna da gwamna mai adalci, Biodun Oyebanji, wanda ke abinda ya dace."
"Idan muka tafi kan ayyukan da gwamna ke yi, ko tantama babu APC ce mai nasara. Haka nan idan muka duba nagartar Tinubu ta isa amsar komai, shi shugaba ne mai share hawaye a siyasance."

Daga Ƙarshe Dai Sunan Ɗan takarar Da Wike Zai Marawa Baya Ya Bayyana

A wani labarin kuma Bisa ga dukkan alamu gwamna Wike na jihar Ribas ya gama yanke shawara kan ɗan takarar da zai marawa baya.

A watan farko na shekar mai kamawa, gwamnan Ribas jagoran tawagar G5 ya sha alwashin bayyana ɗan takarar shugaban kasan da zai wa aikin yakin neman zaɓe a 2023.

Tsagin G5 PDP na takun saka da ɗan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar kan shugabancin Iyorchia Ayu.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Cigaba da Sakin Hannu, An Raba Kyautar Miliyoyi da Ya Je Kamfe a Katsina

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262