Rikicin PDP: Dalilin Da Ka Iya Sa Atiku Ya Rasa Kuri’un Kano a Zaben 2023
- Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP na iya rasa damar kawo jihar Kano a zaben 2023
- Bayyanar Muhammed Sani Abacha, wanda Atiku da kwamitin NWC na PDP basa so a matsayin dan takarar gwamnan jam'iyyar a jihar babban barazana ce ga takarar Atiku
- Wata babbar kotun tarayya a Kano ta ayyana Abacha a matsayin sahihin dan takarar PDP a zaben gwamnan 2023 a jihar
Kano - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar na iya rasa kuri'u masu yawa a Kano a babban zaben 2023.
Jihar Kano na daya daga cikin wurare masu yawan kuri'u a Najeriya da suka samar da kuri'u fiye da miliyan 2 cikin masu zabe miliyan 5 da ke da rijista a yayin zaben 2019.
Shin Atiku zai kawo kuri'un Kano a zaben 2023?
Koda dai Buhari ya kawo jihar a 2019 inda ya samu kuri'u fiye da miliyan 1 cikin kuri'u miliyan 2 zai yi wuya Atiku ya kawo jihar a zaben 2023.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A ranar Alhamis, 22 ga watan Disamba, wata babbar kotun tarayya a jihar ta ayyana Muhammed Abacha a matsayin sahihin dan takarar gwamna na PDP a Kano, jaridar The Guardian ta rahoto.
Justis A M Liman na kotun ya umurci hukumar zabe na kasa mai zaman kanta (INEC) ta dauki Abacha sannan ta wallafa sunansa a matsayin dan takarar gwamnan PDP a Kano a zaben 2023.
Halin da ake ciki game da Atiku Abubakar, PDP da Muhammed Sani Abacha a zaben 2023
Hukuncin wanda aka zartar ya hana Sadiq Wali daukar kansa a matsayin dan takarar gwamnan PDP a Kano.
Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Kori Wali, Ta Tabbatar Da Abacha A Matsayin Dan Takarar Gwamnan Jihar Kano A PDP
Sai dai kuma, Atiku da kwamitin aiki na PDP ya dauki Wali a matsayin dan takarar gwamnan jam'iyyar a Kano.
Wannan ci gaban ya jefa damar da Atiku ke dashi a jihar Kano a zaben 2023 cikin hatsari domin dai bai taba goyon bayan kudirin Abacha ba.
Alkalin ya zartar cewa kuri'un da aka kadawa Abacha a yayin zaben fidda gwanin da tsagin Sagagi ya gudanar a jihar yana bisa doka, rahoton Daily Trust.
PDP ta rasa mambobinta da dama a jihar Plateau
A wani labarin kuma, Umar Mantu, jigon PDP kuma da ga tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ibrahiim Mantu ya dauya sheka zuwa jam'iyyar APC.
Hakazalika, mambobin PDP 20,000 sun sauya sheka zuwa jam'iyya mai mulki a kananan hukumomin Mangu da Bokkos.
Asali: Legit.ng