Zaben 2023: Umar Mantu Da Mambobin PDP 20,000 Sun Sauya Sheka Zuwa APC

Zaben 2023: Umar Mantu Da Mambobin PDP 20,000 Sun Sauya Sheka Zuwa APC

  • Gabannin babban zaben 2023, jam'iyyar APC ta yi babban kamu na jigo da mambobin PDP a jihar Plateau
  • Umar Mantu da 'ya'yan babbar jam'iyyar adawa 20,000 sun sauya sheka zuwa jam'iyya mai mulki a kananan hukumomin Mangu da Bokkos
  • Mai magana da yawun APC a jihar Plateau, Mista Sylvanus Namang, ne ya sanar da ci gaban a ranar Lahadi

Plateau - Dr. Umar Mantu, dan tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ibrahim Matu, ya sauya sheka daga jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa All Progressives Congress (APC).

Batun sauya shekar nasa na cikin wata sanarwa da sakataren labaran jam'iyyar APC a jihar Plateau, Mista Sylvanus Namang, ya saki a ranar Lahadi, 25 ga watan Disamba, PM News ta rahoto.

Umar Mantu da mukarrabansa
Zaben 2023: Babban Jigon PDP, Umar Mantu, Ya Sauya Sheka Zuwa APC Hoto: PM News
Asali: UGC

Mantu ya sauya sheka tare da mambobin PDP 20,000

Kara karanta wannan

Babbar Koma Baya Ga Tinubu Yayin Da Yan APC Sama Da 90,000 Da Wasu Suka Tsallaka Zuwa PDP A Jihar Buhari

Sanarwar ta ce Umar ya koma APC a hukumance a gudunmarsa ta Chanso da ke karamar hukumar Magu ta jihar Plateau.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya bayyana cewa dan siyasar ya sauya sheka ne tare da magoya bayan PDP fiye da 20,000 daga kananan hukumomin Mangu da Bokkos, rahoton Independent.

Ya ce:

"Matashin dan siyasar mai kwarjini ya ce ya koma APC ne saboda akwai bukatar kasancewarsa a wurin da ya dace don bayar da gudunmawa ga ci gaban damokradiyya.
"Dawowa na APC zai kara daukaka jam'iyyar domin zan taka rawar gani wajen tabbatar da nasarar jam'iyyar daga sama har kasa a babban zaben 2023."

Dawowar Umar Mantu APC zai karfafa jam'iyyar, Zakari

Da yake tarban Umar, Malam Sadak Zakari, shugaban APC a gudunmar Chanso, ya nuna jin dadinsa a kan ci gaban.

Kara karanta wannan

Jiga-jigan APC Da Dama Sun Yi Watsi Da Tinubu, Sanwo-Olu, Sun Bayyana Goyon Bayansu Ga PDP Ta Atiku, Jandor

Zakari ya ce sauyin shekar zai karfafa APC a gudunmar Chanso, Pyem a karamar hukumar Mangu da ma jihar Plateau baki daya duba ga matsayin mai sauya shekar.

Kwamishinan muhalli na jihar, Mista Elisha Shehu, ya jinjinawa Umar kan wannan mataki da ya dauka na watsar da PDP da kuma zabar APC.

Kwamishinan ya bayyana cewa duba ga matsayinsa a PDP, shigowarsa APC tabbacin nasara ne garesu a dukkan matakai, domin zai yi amfani da gogewarsa a siyasa cikin jam'iyyar.

APC za ta lashe zabe a jihar Zamfara, Buhari

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce yana da yakinin cewa al'umman jihar Zamfara za su sake zaban jam'iyyar APC a zaben 2023 mai zuwa.

Buhari ya yiwa al'umman kasar albishir da samun gagarumin sauyi idan har Asiwaju Tinubu na APC ya lashe zaben shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng