Takun Saƙa: Kace-Nace Ya Ɓarke Tsakanin Gwamna Wike Da Tsohon Shugaban PDP
- Tsohon shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa yayi martani mai zafi kan gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike
- Tsohon shugaban yace ko kaɗan ba wanda ya isa ya cewa mutanen jihar Ribas ga wanda zasu zaɓa cikin ƴan takarar shugaban ƙasa
- Gwamna Wike ya daɗe yana takun saka tsakanin sa da Atiku Abubakar da shugaban PDP na ƙasa, Iyorchia Ayu
Tsohon shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Prince Uche Secondus, ya bayyana cewa zai yi matuƙar wahala wani mutum ya ƙaƙabawa mutanen jihar Ribas ɗan takarar shugaban ƙasan da za su zaɓa.
Secondus yace mutanen jihar a koda yaushe jam'iyyar PDP suke zaɓa, sannan idon su ya buɗe ta yadda ba wanda ya isa ya tilasta musu zaɓar wani ɗan takarar shugaban ƙasa na wata jam'iyya a zaɓen dake tafe. Jaridar Punch ta rahoto.
Secondus yana martani ne akan wani furuci da gwamna Nyesom Wike yayi a ranar Alhamis, inda yake cewa zai bayyana ɗan takarar sa na shugaban ƙasa a zaɓen watan Fabrairu dake tafe.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A lokacin da yake yaƙin neman zaɓe ga ɗan takarar gwamnan PDP a jihar, Wike yace nan bada daɗewa ba zai gayawa mutanen jihar ɗan takarar shugaban ƙasar da za su kaɗa wa ƙuri'un su.
Gwamna Wike da wasu fusatattun ƴan jam'iyyar PDP da suka kafa wata tawaga ta daban dai suna ta takun saka da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar, Atiku Abubakar da shugaban jam'iyyar na ƙasa, Iyorchia Ayu.
Sun dai haƙiƙance cewa lallai sai Ayu ya sauka daga kan muƙamin sa sannan zasu goyi bayan jam'iyyar a zaɓen shugaban ƙasa. Haka kuma suna buƙatar cewa lallai dole mulki ya koma Kudancin Najeriya a 2023.
Gwamnan PDP Ya Koka Kan Rashin Su Wike a Wurin Yaƙin Neman Zaɓe
A wani labarin kuma shugaban kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP ya koka kan rashin gani su Wike a wurin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam'iyyar.
Gwamna Emmanuel Udon wanda shine shugaban kwamitin ya bayyana cewa yana matuƙar jin zafin rashin gani gwamna Wike da ƴan tawagar sa a wurin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa.
Asali: Legit.ng