Gwamnan PDP Ya Koka Kan Rashin Su Wike A Wurin Yakin Neman Zaɓe
- Shugaban kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na PDP ya nuna damuwar sa kan rashin samun goyon bayan su Wike
- Tawagar G5 na nan akan bakanta na cewa lallai dole sai Ayu yayi murabus daga kan shugabancin jam'iyyar
- Gwamnan Wike yayi alƙawarin bayyana inda akalar sa za ta koma game da takarar shugaban ƙasa nan bada jimawa ba
Gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel, ya bayyana cewa abin na yi masa ciwo cewa gwamnonin PDP biyar na G5 basa tare da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam'iyyar, jaridar Premium Times ta rahoto.
Mr Emmanuel dai shine shugaban kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP.
A yayin wata ziyara da gwamna Ortom ya kai jihar Akwa Ibom, gwamna Emmanuel ya bayyyana cewa:
Zaka waiga wajen yaƙin neman zaɓe, ba zaka gansu ba, nan da nan sai ka ji kana buƙatar su. Waɗannan mutane ne da kuka faro tare, har yanzu ina tunanin bana jindaɗi cewa ba mu tare a wajen yaƙin neman zaɓe.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Mr Ortom mamba ne a G5, wacce ke ƙarƙashin jagorancin gwamna Wike na jihar Ribas.
Sauran gwamnonin da suke mambobi ne a tawagar sun haɗa da Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu), Okezie Ikpeazu (Abia), da Seyi Makinde (Oyo).
Tawagar wacce aka kafa ta jim kaɗan bayan zaɓen fidda gwanin ɗan takarar shugaban ƙasa a watan Mayu, har ya zuwa yanzu ta ƙi marawa Atiku Abubakar baya.
Tawagar ta G5 a watan Nuwamba a jihar Abiya, ta bayyana cewa za ta goyi bayan ɗan takarar da ya fito ne daga Kudancin Najeriya a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023.
Gwamna Wike yayi alƙawarin cewa a watan Janairu zai bayyana ɗan takarar da zai marawa baya a zaɓen shugaban ƙasa.
Tawagar dai tana ta fafutukar neman ganin cewa shugaban PDP na ƙasa, Iyorchia Ayu, ya yi murabus domin ɗan Kudancin Najeriya ya shugabanci jam'iyyar saboda a samar da daidaito.
Wani Babban Ƙusa a PDP Ya Sauya Sheƙa Zuwa APC a Jihar Sokoto
A wani labarin kuma jam'iyyar PDP tayi wani babban rashi inda wani babban jigonta ya fice daga jam'iyyar zuwa jam'iyyar APC a jihar Sokoto. Alhaji Yusha'u Kebbe yace sam jam'iyyar ta kasa yin kataɓus a jihar.
Tsohon ƙusar na jam'iyyar PDP ya bayyana cewa sai da ya tattauna da magoya bayan sa na dukkanin ƙananan hukumomin jihar kafin ya yanke wannan hukuncin na sauya sheƙar zuwa jam'iyyar APC.
Asali: Legit.ng