Ana Zargin Shugaban Majalisa da Cin Amanar Tinubu da Yi Wa Atiki aiki a Zaben 2023
- Kwamitin yakin zaben Asiwaju Bola Tinubu ya wanke Dr. Ahmad Lawan daga zargin da ake yi masa
- Magoya bayan Hon. Bashir Machina sun jefi Lawan da zargin goyon bayan PDP a zaben shugaban kasa
- Festus Keyamo ya karyata zargin nan, ya ce tun fil azal Sanatan bai taba marawa jam’iyyar PDP baya ba
Abuja - Kwamitin neman takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya yi amanna da shugaban majalisar dattawan Najeriya, Dr. Ahmad Lawan.
Punch ta rahoto kwamitin yana cewa ya gamsu Ahmad Lawan ba zai taba cin amanar jam’iyya ba, hakan kariya ne daga zargin 'yan adawa.
Kwamitin yakin neman zaben Hon. Bashir Machina ya zargi magoya bayan Lawan da fadan kalamai marasa dadi a kan Asiwaju Bola Tinubu.
A wata sanarwa daga bakin Festus Keyamo, an maida martani ga Husaini Isa wanda Darektan yada labarai ne a kwamitin takarar zaben Machina.
Anya Lawan zai yaudari Tinubu - Festus Keyamo?
Kakakin kwamitin neman zaben shugaban kasa na APC, Festus Keyamo ya ce an yarda da Lawan.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Keyamo ya na mamakin yadda magoya bayan Hon. Machina za su kai su na zargin shugaban majalisar dattawa da yi wa jam’iyyarsa zagon-kasa.
Jawabin Kakakin APC PCC
“Tun 1999, Lawan yake adawa ga jam’iyyar PDP. Saboda haka duk wanda a dare daya zai ce Lawan da mutanensa suna yi wa PDP aiki ne, ya duba lafiyarsa.
Mutum ne shi mai hakuri. Ba na tunanin Machina da mutanensa za su iya yi masa wannan kamar yadda ake ikirari. APC tsintsiya madaurin ki daya ce.
Masu yada wadannan rade-radi ‘yan jam’iyyar PDP ne, sun saba kawo soki-burutsu.
Damar da PDP take da shi na lashe zaben 2023 shi ne kurum ta ce mutane ba su tare da APC. Duk karya ce, karyar banza, jam’iyya ta na natsu da Lawan.”
Ana neman raba kanmu - APC
Pulse ta rahoto Darektan yada labaran APC, Bala Ibrahim yana tabbatar da ra’ayin PCC. A cewarsa Lawan yana goyon bayan Tinubu tun da ya sha kasa a zabe.
Ibrahim ya nuna takaicinsa a kan abin da yake faruwa, ya zargi wasu da yin aiki tukuru domin ganin sun samar da baraka a tafiyar jam’iyyar APC mai mulki.
ACC ta bi 'dan takaran NNPP
An ji labari a baya cewa shugaban Kungiyar Abia Christian Community (ACC) ya ce 'dan takaran Jam’iyyar NNPP za su zaba a zaben Gwamna da za ayi a 2023.
Shugaban ACC, Apostle Reminder C. Gad ya ce za su dage sosai wajen ganin Dr. Ukpai Iro Ukpai ya zama Gwamna a jam’iyya mai kayan marmari a jihar ta Abia.
Asali: Legit.ng