2023: Ku Zabi Mutum Nagari Ba Wai Jam'iyya Ba, Gwamna Ortom Ga Yan Najeriya

2023: Ku Zabi Mutum Nagari Ba Wai Jam'iyya Ba, Gwamna Ortom Ga Yan Najeriya

  • Gwamnan jihar Benuwai ya shawarci mazauna su zabi cancanta a babban zabe mai zuwa kar su tsaya duba jam'iyya
  • Samuel Ortom, mambam tawagar G5 a PDP, yace a halin yanzu mutane na bukatar masu taimaka masu ne
  • Gwamna Ortom ya rattaba hannu kan kundin kasafen 2023 na jiharsa bayan majalisar dokoki ta amince

Benue - Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai dake arewa ta tsakiya ya rattaɓa hannu kan kasafin kuɗin 2023 da ya kai Biliyan N179.5bn ya zama doka.

Jaridar Punch ta rahoto cewa Ortom ya sa hannu kan kasafin ne a ɗakin taron gidan gwamnati dake Makurdi, babban birnin jihar Benuwai ranar Alhamis 22 ga watan Disamba, 2022.

Samuel Ortom.
2023: Ku Zabi Mutum Nagari Ba Wai Jam'iyya Ba, Gwamna Ortom Ga Yan Najeriya Hoto: Samuel Ortom
Asali: Facebook

Yayin bikin sa hannun, Ortom ya miƙa godiyarsa ga mambobin majalisar dokoki bisa goyon baya da hanzarin kammala aiki kan kasafin kuma suka amince suka dawo wa da tsagin zartaswa.

Kara karanta wannan

Bukola Saraki Ya Gargadi Hukumomin Tsaro Kan Batun Gwamnan CBN

Gwamnan yace, "Muna yaba wa majalisar dokoki ta 9 bisa haɗin kansu da fahimtar juna wanda ya taimaka mana wajen samun nasarori."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Duk da 2023 mace ce da ciki kuma maƙare da kaya, muna fatan Allah ya taimake mu muga bayan kalubalen da muke fama da su. Da yawanmu muna tsammani komai zai sauya."
"Mu mutane ne kamar kowa mun yi bakin kokarin mu kuma muna fatan Allah da kansa zai cece mu, ya bamu zaman lafiya da fata nagari da duk abinda zai sa mu ji daɗin shekara mai zuwa."

Abinda ya kamata mutane su duba lokacin zaɓe - Ortom

Da yake tsokaci kan zaɓe mai zuwa, gwamna Ortom ya roki mazauna jihar Benuwai su zaɓi mutane masu amana kar su tsaya duba jam'iyyu.

A rahoton Vanguard, Ya kara da cewa:

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya Tace Batun Gwamnan Babban Banki Yana Gaban Kotu, Dan Haka Ita Nata Sa Ido

"Idan zaɓen 2023 ya zo, mu yi aiki tukuru kana mu zabi cancanta ba jam'iyya ba. Ya zama wajibi mu san su wa zamu ba amana waɗanda zasu taimake mu da ƙasar mu."
"Mu sanya gaskiya a zukatan mu a duk lokacin da zamu zauna yin nazari kuma muna fatan Allah ya shige mana gaba."

A wani labarin kuma Hukumar zabe ya kasa INEC tace akwai yan Najeriya da dama da za'a haramtawa zaɓe saboda wasu dalilai a 2023

Hukumar zabe INEC ta gargadi 'yan siyasan dake sayen katunan zabe su shiga taitayinsu, tace suna adashen da babu kwasa.

INEC tace ta bullo da fasahar zamani domin ko kazo da katin zaɓe da yuwuwar ba zaka jefa kuri'a ba idan abu 2 ba su yi kama da kai ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262