Gudaji Kazaure: Majalisa ta Nesanta Kan ta daga Zargin Satar Naira Tiriliyan 89 a CBN
- Shugaban Majalisar wakilan tarayyan Najeriya ya yi magana kan kwamitinsu Muhammad Gudaji Kazaure
- Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya ce babu abin da ya hada ‘yan majalisa da aikin da su Gudaji Kazaure suke yi
- Gbajabiamila ya nuna ‘yan majalisa ba su da ikon shiga hurumin kwamitin da shugaban kasa ya kafa shi
Abuja - Majalisar wakilan tarayya ta ce ba za ta iya hana Muhammad Gudaji Kazaure aikin binciko zargin badakalar kudi da aka tafka a bankin CBN ba.
The Cable ta ce Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya yi wannan bayani ne ga manema labarai bayan ya gana da Mai girma shugaban Najeriya a fadar Aso Villa.
Hon. Muhammad Gudaji Kazaure yana ikirarin kwamitinsu ya gano wasu kudi da aka karkatar a bankuna. Fadar shugaban kasa ta musanya zargin nan.
A matsayinsa na shugaban majalisar wakilan tarayya, Gbajabiamila ya ce ba su da hurumi a kan ‘aikin’ da aka ba Kazaure, domin bai shafi majalisa ba.
Babu ruwanmu a maganar - Gbajabiamila
Rt. Hon. Gbajabiamila yake cewa ‘yan majalisar tarayya za su iya tsoma bakinsu ne idan Kazaure ya yi amfani da karfinsa, ya murkushe ‘yan kwamitinsa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An rahoto Gbajabiamila yana cewa ba daga majalisar wakilan kasar nan zargin da Gudaji Kazaure yake yi, ya samo asali ba, ya ce wannan ba aikinsu ba ne.
"Babu abin da ya hada wannan da majalisar tarayya. Babu abin da na sani a kai. Ba da matsayar majalisar tarayya aka dogara ba.
Ba daga wata tattaunawa a majalisa ya dauko asali ba. Nayi imani ya ce bangaren zartarwa ya ba shi hurumin yin aikin da yake yi.
Idan har haka abin yake, babu ruwan majalisar tarayya. Inda kawai majalisa za ta sa baki shi ne idan har ya taba mutucin majalisa."
- Rt. Hon. Femi Gbajabiamila
Gbajabiamila ya ce da suka tuntubi wasu ‘yan kwamitin da Kazaure yake Sakatare, an fada masu shugaban kasa ya rusa kwamitin ko makamancin haka.
A rahoton Punch, shugaban majalisar ya fadawa manema labarai a ranar Talata cewa nauyin binciken da yake cewa yana yi, yana hannun Kazaure.
Garba Shehu ya shaida cewa an ruguza kwamitin nan da ‘Dan majalisar mai wakiltar mazabun Roni, Gwiwa, Yankwashi da Kazaure yake takama da shi.
Atiku a Katsina
Labari ya zo cewa da ya gama sauraron kalaman Atiku Abubakar a fadarsa, Sarkin Katsina, Dr. Abdulmumin Kabir Usman ya hango nasara a tattare da shi.
Mai martaba Dr. Abdulmumin Kabir Usman ya ce a matsayinsa na Uban al’umma, iyakarsa da 'dan takaran na PDP shi ne yi masa addu’a a zabe mai zuwa.
Asali: Legit.ng