Atiku Ya Je Kamfen Zuwa Jihar Su Buhari, Yayi Alkawarin Bude Duk Kan Iyakoki Kasar Nan
- Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP ya bayyana abin da ya shirya yiwa 'yan Najeriya idan ya gaji Buhari
- Atiku ya ce zai bude iyakokin kasar nan, kuma zai warware dukkan matsalolin da suke tattare da kungiyar malaman jami'a ta ASUU
- Atiku ya sha bayyana manufarsa ta gyara tattalin arzikinda kuma habaka ilimi; ciki har da daidaita lamarin ASUU
Jihar Katsina - Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana kadan daga shirinsa idan aka zabe shi a zaben 2023.
Atiku ya bayyana cewa, yana da nufin bude iyakokin kasar nan domin ci gaba da shigo da kayayyaki sabanin yadda gwamnatin APC ta yi.
Ya bayyana hakan ne a filin wasanni na Muhammadu Dikko da ke Katsina, kwanaki 66 kafin zaben 2023.
Da yake jawabi, Atiku ya yi alkawarin cewa, zai magance matsalolin tsaro kana ya inganta tattalin arzikin kasar nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakazalika, batun yajin aikin malaman jami'a, Atiku ya ce zai tabbatar da ya biya musu bukatunsu tate da warware dukkan matsala.
A cewarsa:
"Duk wani ci gaba da kuke gani a Katsina, an samar dashi ne a mulkin PDP ciki har da wannan filin wasan, da ma sabon gidan gwamnati."
Yadda aka yi kamfen din PDP a Katsina
Abokin takarar Atiku, Ifeanyi Okowa da shugaban PDP na kasa, Iyorchia Ayu na daga cikin wadanda suka halarci wannan taro na gangamin PDP.
Tawagar kamfen din Atiku dai ta isa jihar ne da misalin karfe 2:07 na rana, kuma ta samu tarbar dan takarar gwamnan PDP a jihar, Yakubu Lado Dan Marke da abokin takararsa, Arch. Ahmed Aminu Yar'adua.
Hakazalika, akwai darakta janar na tawagar gangamin kamfen din Atiku/Lado, Mustapha Inuwa da dai sauran jiga-jigai da magoya bayan PDP.
Atiku ne ya yada hotunan ziyarsa a jihar Katsina a shafinsa na Twitter.
Atiku ya ziyarci mahaifiyar marigayi Yar'adua
Lokacin da suka iso, Atiku da tawagarsa sun ziyarci mahaifiyar marigayi tsohon shugaban kasa, Alhaji Umaru Musa Yar'adua da kuma mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman.
Ana kyautata zaton Atiku zai kaddamar da shugabannin kwamitin gangamin Atiku na Atiku 5-Point Agenda Awareness Forum.
Asali: Legit.ng