Mun Binne Batun Hada Maja, Kofar NNPP A Bude Take Ga Masu Sauya Sheka, Mataimakin Kwankwaso
- Abokin takarar Rabiu Kwankwaso a jam'iyar NNPP, Isaac Idahosa, yace sun rufe zancen haɗa maja da wasu jam'iyyu
- Sai dai a yanzu za'a zuba idona gani ko jam'iyyar NNPP zata kai bantenta a babban zaɓen shugban kasa kamar yadda wasu ke ikirari
- Tsohon gwamnan Kano, Sanata Kwnakwaso ne ke neman zama shugaban kasa a jam'iyyar tare da abokin gaminsa, Idahosa
Lagos - Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar NNPP, Isaac Idahosa, ya kore duk wata yuwuwar kulla ƙawance da wata jam'iyya gabanin zaben 2023.
Amma abokin gamin tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso, ya jaddada cewa ƙofar jam'iyyar NNPP a buɗe take ga duk masu son shigowa a dama da su.
Idahosa ya yi wannan furucin ne a cikin shirin Politics Today ta kafar Talabijin ɗin Channels tv ranar Litinin, 19 ga watan Disamba, 2022.
Ɗan takarar ya kara da cewa NNPP na da kwarin guiwar zata lashe zaben shugaban ƙasa a 2023.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Idahosa ya ce:
"Ya rage ga sauran jam'iyyun dake son kulla kawance da NNPP, bamu ke nema ba. Zancen maja ya kare kamar yadda kowa ya sani amma duk masu son shigowa cikin mu kofar mu a bude take."
"Kofar mu a bude take ga masu son haɗa karfi da mu domin tabbatar da mun kafa gwamnatin al'umma, wannan shi ne fatan mu Kuma muna maraba da kowa."
Idahosa, Bishof a majami'ar Illumination Assembly da ke Ajah, jihar Legas ya ce NNPP ta samu karɓuwa a wurin 'yan Najeriya a dukkanin sassan ƙasar nan, musamman daga tushe.
Abokin takarar Rabiu Musa Kwankwaso yace Najeriya zata gyaru idan ta samu jagora wanda ba maganar baki kaɗai yake ba, yana tafiya ne a kan maganganunsa.
Ɗan takarar gwamnan Katsina ya kara karfi
A wani labarin kuma APC Ta Samu Gagarumin Goyon Baya Yayin Da Jam'iyya Guda Ta Rushe Zuwa Cikinta a Katsina
Jam'iyya mai mulki ta samu wannan ci gaban ne yayin gangamin yakin neman zaɓen ɗan takarar gwamna a inuwar APC, Dikko Umaru Radda, wanda ya gudana a Ingawa.
An tattaro cewa zagayen kamfen Radda a yankunan shiyyar Daura cike yake da tarban masu sauya sheka a garuruwa da dama.
Asali: Legit.ng