Dan Allah Kada Ka Bamu Kunya, Yaro Dan Shekaru 10 Ya Roki Peter Obi a Bidiyo
- An gabatar da wani roko a gaban Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na Labour Party gabannin zaben 2023
- Yaro dan shekara 10, Efosa Osadebamwen ne ya roki Obi a cikin wani bidiyo da mahaifinsa ya saki a YouTube
- Efosa ya roki tsohon gwamnan na jihar Anambra da ya tabbata bai ba miliyoyin yan Najeriya da suka yarda da shi kunya ba idan ya zama shugaban kasa
Abuja - Wani yaro dan shekaru 10 mazaunin babban birnin tarayya Abuja ya aike sako ga dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party a zaben 2023, Peter Obi.
Yaron mai suna Efosa Osadebamwen ya ce ya aminta kuma ya yarda cewa tsohon gwamnan na jihar Anambra zai kawo mafita ga matsalolin da suka addabi Najeriya.
A wani bidiyo da mahaifin Efosa ya wallafa a YouTube, matashin yaron ya roki Peter Obi da ya tabbata bai gazawa yan Najeriya ba idan har aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a 2023.
Kalamansa:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Ya mai girma Peter Obi, na yarda da kai yallabai. Kuma dan Allah, kada ka gaza mana mu yan Najeriya saboda yan Najeriya sun dogara da kai."
Da aka tambaye shi wa ya fada masa yan Najeriya sun dogara ne a kan Peter Obi, Efosa ya ce ya yarda Obi zai yi aiki fiye da sauran yan takarar shugaban kasa na 2023.
Ya kara da cewar:
"Saboda na yarda da Peter Obi."
Duk da karancin shekarunsa ya tabbata Efosa na cikin yan Najeriya da dama da ake yiwa lakabi da 'Obidients' sakamakon goyon bayan dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party.
Kalli bidiyon Efosa yana rokon Obi a kasa:
Da yake magana ga Legit.ng, mahaifin Efosa ya ce dansa ya kai shi iya wuya, inda ya nace cewa yana da sako zuwa ga Peter Obi.
Ya ce:
"Yana ta damuna cewa yana so ya aika sako ga Peter Obi. A takaice, yana da yanci kan abun da ya yarda da shi.
"Na fada masa ba zai iya kada kuri'a ga Obi ba, saboda shi yaro ne kuma bai da katin zabe. Ya ce ya sani amma fatansa shine Obi ya yi nasara."
Ya ci gaba da cewa:
"Kuma kada ya ba mutane kunya, ina tsoro. Da na gama bidiyon sai na ce, dole na fitar da shi idan ya isa ga Obi, ya san cewa wasu iyayen YouTube na kallo, yaran na kallo su ma."
Asali: Legit.ng