Ba Zan Taba Shiga Lamarin Mulkin Sabon Gwamna ba, Mai Rusau

Ba Zan Taba Shiga Lamarin Mulkin Sabon Gwamna ba, Mai Rusau

  • Gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-Rufai ya ce bazai shiga lamarin mulkin, sannan zai tattara komatsansa ya bar jihar da zarar ya mika ga gwamna mai jiran gado
  • Ya ce, Ubangiji shi ne zai yi jagora ga gwamna mai zuwa, duk da yana da tabbacin Uba Sani zai lashe zaben shekara mai zuwa
  • Ya kara da cewa, 'dan takarar gwamnan APC mutumin kirki ne, kuma zai jagoranci mutanen jihar, saboda ya san shi sama da shekaru 20

Kaduna - Gwamnan Nasiru El-Rufai na jihar Kaduna ya ce zai tattara komatsansa ya bar Kaduna a ranar 29 ga watan Mayu, 2023 bayan mika mulki ga magajinsa, yadda ba zai tsoma baki a mulki na gaba ba.

Gwamnan wanda ya bayyana tabbacin cewa Sanata Uba Sani ne zai gajesa, ya ce ba zai bada wata gudunmawa a gwamnatin jam'iyyar APC mai zuwa ba, Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Guri/Malam Madori: Tinubu Zai Taimaka Wajen Hako Danyen Man da Ake da Shi a Arewa

Mai Guduma
Ba Zan Taba Shiga Lamarin Mulkin Sabon Gwamna ba, Mai Rusau. Hoto daga vanguardngr.com
Asali: UGC

Uba Sani mutumin kirki ne

El-Rufai ya ce Ubangiji zai yiwa gwamna mai jiran kujera jagora idan yana da zuciya mai kyau, inda ya kara da cewa Sanata Uba Sani mutumin kwarai ne wanda zai jagoranci jama'an jihar yadda ya dace.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya siffanta Sanata Uba Sani a matsayin wanda ya dace ya gaje shi, wanda zai kai jihar Kaduna matsayin da yafi na yanzu idan aka zabesa a matsayin gwamna.

Gwamnan, wanda ya zanta a wani taron anguwa da yanki na tsakiya suka shirya ranar Litinin, ya ce ya san sanatan sama da shekaru 20 kuma ya tabbatar da gogewarsa a siyasance.

El-Rufai ya shawarci mutanen jihar Kaduna da kada su shigar masa da yasa baki Uba Sani, ya basu mukamai ko kwangiloli idan ya zama gwamna.

Sanata Uba Sani yayi martani

Kara karanta wannan

Gwamna ya Umarci a Damke Kukun da Tayi Abincin Liyafar Kirsimati da ya Shirya, Yace Babu Dadi

Yayin jawabi a taron, Sanata Uba Sani ya bayyana yadda ya zama dalibin Malam Nasiru El-Rufai a makarantar gwamnati da siyasa a shekaru 20 da suka shude, sakamakon haka yayi "digiri" da dama.

"A wannan makarantar, an yi wasu mutane da suka shigo kafin ni, mutane irinsu sakataren gwamnatin jihar, Malam Balarabe Abbas Lawal, wanda ya girme ni. Sai dai, makarantar babu ranar gama ta. Soboda haka, har yanzu muna koya ne."

- A cewarsa.

"Kafin zuwan wannan gwamnatin, tagomashin gwamnatin ana kasafta shi ne ga wasu 'yan kalilan din mutane masu ruwa da tsaki, bayan biyan albashi. Saboda haka, babu wani abu da ya saura don cigaba, duk da irin tarin arzikin da jihar Kaduna ke amsa daga gwamnatin tarayya.
"Amma Malam Nasiru El-Rufai ya canza labarin ta hanyar bunkasa ilimi, harkar lafiya da samar da ababen more rayuwa wanda mutanen kwarai na jihar Kaduna ke amfana, maimakon wasu tsirarun mutane."

Kara karanta wannan

El-Rufai: Abubuwa 2 da ya Zama Wajibi Magajin Buhari Ya Yi Yaki da Su a Mulki

- A cewarsa.

'Dan takarar gwamnan ya ce sakamakon kudin da aka narka a bangaren ilimi ya sa aka fara gurbar abun da aka shuka, saboda jihar Kaduna ita ce jiha ta hudu a kasar wacce dalibai sukafi lashe jarabawar kammala sakandiri duk da darussan Turanci da Lissafi.

Uba Sani ya ce gwamnati ba zata iya daukar ragamar ilimi ita kadai ba, inda yayi kira ga masu hannu da shuni da su tallafa ga dalibai haifaffun jihar Kaduna zuwa jami'a.

A cewarsa, cikin kwanakin nan ya bawa dalibai 280 na makarantun gaba da sakandiri tallafi don taimaka musu cigaba da karantunsu.

Har ila yau, ya kara da cewa gwamna El-Rufai ya tallafawa 'yan kasuwa, ta hanyar wani tsari da zasu biya su mallaki shagunansu.

Ya tuna da yadda aka mika shagunan ga manyan ma'aikatan gwamnati da sarakuna a baya, wadanda su kuma suke bada hayarsu ko siyarwa 'yan kasuwa kan farashi mai tsadar gaske.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng