Kotu Ta Rushe Zaben Fidda Gwanin PDP, Ta Ayyana Halartaccen Ɗan Takara a 2023

Kotu Ta Rushe Zaben Fidda Gwanin PDP, Ta Ayyana Halartaccen Ɗan Takara a 2023

  • Kotun ɗaukaka kara mai zama a Abuja ta maida wa Lawal Usman tikitin takarar Sanatan Kaduna ta tsakiya a PDP
  • Kwamitin alƙalai ukun sun yanke jingine hukuncin ƙaramar Kotu, wacce ta umarci PDP ta sake sabon zaben fidda gwani
  • Ibrahim Usman ne ya kalubalanci nasarar Lawal Usman a Kotu, bayan canza zabe ya samu nasara da kuri'u 210

Abuja - Kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Abuja ta ayyana Lawal Usman a matsayin sahihin ɗan takarar jam'iyyar PDP a mazaɓar Sanatan Kaduna ta tsakiya a 2023.

Channels tv tace Kotun ta jingine hukuncin babbar Kotun Kaduna, wacce ta umarci jam'iyar PDP ta shirya sabon zaɓen fidda gwani, Ibrahim Usman ya samu nasara.

Kotun daukaka kara.
Kotu Ta Rushe Zaben Fidda Gwanin PDP, Ta Ayyana Halartaccen Ɗan Takara a 2023 Hoto: channels
Asali: UGC

Da yake yanke hukunci, kwamitin Alkalai uku karkashin jagorancin mai shari'a Peter Affen, ya bayyana cewa ƙaramar Kotun da ta umarci a canza zaben ta shiga hurumin da ba nata ba.

Kara karanta wannan

2023: Bayan Sauya Shekar Mambobin PDP, Fitacciyar Jam'iyya Ta Rushe Kanta, Ta Koma APC

Kwamitin Alkalan ya ce Kotun baya ta tsoma baki a harkokin tafiyar da jam'iyya na cikin gida wanda kuma ba ta da hurumin tsoma baki a ciki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yadda shari'a ta kasance a ƙaramar kotun

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa mai shari'a Umar na babbar Kotun tarayya mai zama a Kaduna ya yanke hukunci bisa bukatar, Ibrahim Usman.

Ibtahim Usman, ɗaya daga cikin 'yan takara, ya kalubalanci nasarar da Lawal Usman ya samu a zaɓen fidda ɗan takarar Sanatan Kaduna ta tsakiya a inuwar PDP.

Alkalin ya umarci a canza sabon zaɓen cikin makonni biyu. A zaben ne PDP ta ayyana Ibrahim Usman a matsayin wanda ya samu nasarar zama ɗan takarar Kaduna ta tsakiya da kuri'u 210.

A zaɓen farko kuma da babbar Kotun tarayya ta rushe Lawal Usman ne ya samu nasara da kuri'u 99, ya lallasa abokin hamayyarsa na kusa, Ibrahim Usman wanda ya samu 84.

Kara karanta wannan

Da Dumi-dumi: Tsageru Sun Kaiwa Ɗan Takarar Jam'iyyar APC Hari a Jihar Kano

A halin yanzun, Kotun ɗaukaka ƙara a birnin tarayya Abuja ta tabbatar da ingancin zaɓen farko da Lawal Usman ya samu nasara.

Atiku Ya Bayyana Babban Alkawarin Da Buhari Ya Daukar Masa Kan Zaben 2023

A wani labarin kuma Ɗan Takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP yace Buhari ya ɗaukar masa alkawari game da zaben 2023

Atiku Abubakar yace Buhari ya tabbatar masa da cewa za'ai sahihi kuma gamsasshen zaɓe, bisa haka yake ganin kamar ya zama shugaban ƙasa.

A cewar Atiku ya haɗu da shugaba Buhari sau biyu kan batun zaɓe, don haka yana da yakinin samun nasara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262