Yan Daba Sun Farmaki Ayarin Dan Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya a Inuwar APC

Yan Daba Sun Farmaki Ayarin Dan Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya a Inuwar APC

  • Wasu 'yan daba da ba'a gano ko su waye ba sun farmaki ayarin tawagar kamfen ɗan takarar Sanatan Kano ta tsakiya a inuwar APC
  • A wata sanarwa da hadiminsa ya fitar yau Lahadi, yace akalla magoya baya 17 maharan suka jikkata, suna kwance a Asibiti
  • Bayanai sun nuna cewa lamarin ya faru ne yayin da AA Zaura ya kai ziyarar ta'aziyya ƙauyen Gayawa

Kano - Ɗan takarar Sanatan Kano ta tsakiya a inuwar APC, Abdulsalam Abdulkarim Zaura, ya tsallake rijiya da baya yayin da wasu 'yan Daba suka farmaki ayarin kamfe ɗinsa.

Jaridar Vangauard ta rahoto cewa lamarin ya faru ne ranar Asabar lokacin da AA Zaura ya kai ziyarar ta'aziya ƙauyen Gayawa, ƙaramar hukumar Ungogo.

Abdulsalam Abdulkarim Zaura.
Yan Daba Sun Farmaki Ayarin Dan Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya a Inuwar APC Hoto: vanguardngr
Asali: UGC

An ce 'yan daban sun kaiwa Ayarinsa farmaki ne a kusa da Gadar Katako da ke Rimin Kebe bodar kananan hukumomin Nasarawa da Ungogo a hanyarsa ta dawowa.

Kara karanta wannan

'Dan Majalisar Tarayya Ya Jingine 'Dan Takarar Jam'iyyarsa, Yace Tinubu Zai Wa Aiki a 2023

Mai taimaka wa ɗan takarar ta fannin yaɗa labarai, Ibrahim Mu'azzam, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ranar Lahadi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yace aƙalla magoya baya 17 ne suka ji raunuka a harin kuma yanzu haka suna kwance a Asibitin Murtala Muhammad suna karɓan magani.

Mu'azzam ya ƙara da cewa ɗan takarar Sanatan APC a Kano ta tsakiya ya yi Allah Wadai da harin wanda har yanzun ba'a gano masu hannu ba kuma ya nemi masoyansa su kwantar da hankula.

A cewarsa, "A binciken da aka yi kan ɓarnar da maharan suna tafka an gano mutane 17 ne suka samu karami ko babban rauni. Masu manyan rauni na kwance a Asibitin Murtala Muhammad."

"Zaura ya tabbatarwa waɗanda lamarin ya shafa cewa za'a basu kulawar da ta dace, kuma zamu ɗauki matakin doka kan maharan kuma ina baku tabbacin zasu ɗanɗana kuɗarsu."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Harbe Daraktan Kwamitin Kamfen Atiku A Wata Jiha

Wane mataki aka ɗauka zuwa yanzu?

A halin yanzu, Darakta Janar na kwamitin yakin neman zaɓen AA Zaura, Yahaya Adamu, ya rubuta takardar korafi zuwa ga kwamishinan 'yan sandan Kano.

Ya bukaci hukumomin tsaro su gudanar da sahihin bincike kan harin su zakulo masu hannu domin su girbi abinda suka shuka, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Da aka tuntube shi, kakakin hukumar 'yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna, yace a halin yanzu yana kokarin gano wurin da lamarin ya auku.

A wani labarin kuma Ɗan majalisar tarayya na jam'iyyar ADC daga Kogi ya ayyana goyon bayansa ga ɗan takarar shugaban ƙasa na APC Ɗan majalisar yace bai da mu da duk abinda za'a ce ba, amma Tinubu ya nuna wa duniya zai iya idan aka duba abinda ya yi a Legas.

Ya sanar da matakin da ya ɗauka ne lokacin da ya kai ziyara wurin taron masu ruwa da tsaki na APC a birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

2023: "Ka Ci Zaɓe Ka Ci Zabe" Yadda Dubun Dubatar Magoya Baya Suka Yi Maraba da Tinubu a Jihar Arewa

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262