2023: APC Ta Samu Gagarumin Goyon Baya Yayin Da Jam'iyya Guda Ta Rushe Zuwa Cikinta a Katsina
- Jam'iyyar APC mai mulki a jihar Katsina na ci gaba da cin karenta babu babbaka yayin da shiri ya yi nisa kan zaɓen 2023
- Tururuwar sauya shekar mambobin manyan jam'iyyu kamar PDP da NNPP ya ƙara wa inuwar APC karfi a Katsina
- Bugu da ƙari, jam'iyyar PRP reshen jihar ta rushe tsarinta cikin APC domin goyon bayan Dakta Dikko Umaru Radda
Katsina - Jam'iyyar All Progressive Congress (APC) mai mulkin jihar Katsina ta samu gagarumin ƙarin goyon baya yayin da ake tunkarar babban zaɓen 2023.
A wani rahoto da jaridar Independent ta tattara, jam'iyyar PRP reshen jihar ta rushe tsarinta kuma ta sha alwashin ƙulla ƙawance da goyon bayan ɗan takarar gwamna a APC, Dikko Umaru Radda.
Shugaban PRP, Dr. Ahmad Alhassan, shi ne ya bayyana haka a Ingawa yayin gangamin yakin neman zaɓen ɗan takarar gwamna na APC.
Da yake jawabi, Shugaban PRP yace sun zabi goyon bayan APC ne saboda kudorori da manufofin jam'iyyun biyu sun yi kama gabanin zaɓen 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ɓangarensa, ɗan takarar gwamnan Katsina a APC, Dakta Radda, ya roki masu katin zabe su goyi bayan tazarce kana su kaɗa wa jam'iyyar kuri'unsu a zabe mai zuwa.
A gangamin karamar hukumar Mani kuma, Radda ya nuna damuwa kan rashin kayan walwala musamman ruwan sha mai tsafta a kauyukan yankin.
Nan take ɗan takarar ya ba da umarnin gina masu rijiyoyin burtsatse domin samar da ruwan sha ga talakawan yankin kuma ya sha alwashin sanya musu Turansufoma domin su ci gaba da ganin haske.
Bugu da ƙari, Dakta Radda ya ba da kyautukan Babura a kamfen Kankiya. Baburan sun isa hannun kwamitin 'Yan sa'kai a a fadar Hakimi don kara inganta tsaro.
Ya ce ya ɗauki matakin baiwa kwamitin tsaron Babura ne domin suna taka nuhimmiyar rawa wajen inganta tsaro a Kankiya.
Dakta Radda ya kuma roki masu kaɗa kuri'a da su zabi ɗan takarar shugaban kasa a inuwar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Kwamitin kamfen Dikko/Jobe ya tabbatar
Legit.ng ta tuntubi mamban kwamitin yakin neman zaɓen APC a jihar Katsina, Anas Jobe Aliyu kuma ya tabbatar da faruwar lamarin.
Anas Aliyu ya shaida wa wakilinmu cewa jiga-jigan PRP da suka haɗa da shugabanni, 'yan takara da magoya baya ne suka sauya sheka zuwa APC a wurin taron.
Yace:
"Eh tabbas haka ne, shugabannin PRP, 'yan takara da mambobi duk sun dawo APC a Ingawa. Wato a duk zagayen da muke yi a kananan hukumomin shiyyar Daura, kusan ko ina sai an samu masu sauya sheka."
"Mutane sun fara fahimtar kudirorin Dikko Radda kuma sun amince shi ne zaɓinsu a 2023. A halin yanzun mun gama kamfen a shiyyar zamu huta kafin tafiya wata shiyyar."
A wani labarin kuma Jam'iyyar PDP ta zauna zama sulhu da tsagin Gwamna Wike a Patakwal domin dinke ɓarakar cikin gida
Sai dai wasu majiyoyi sun bayyana cewa an tashi zaman ba tare da fahimtar juna ba kasancewar tawagar G5 suɓ kafe dole sai Ayu ya yi Murabus.
Tuni dai alamu suka nuna cewa Atiku ya manta batun tsagin G5 ya ci gaba da harkokinsa, ya maye gurbin Makinde da gwamna Adeleke na jihar Osun.
Asali: Legit.ng