Jam'iyyar PDP Ta Rasa Daruruwan Mambobinta a Gundumar Tsohon Gwamnan Jigawa
- Jam'iyyar PDP ta tafka asarar mambobinta a gundunar tsohon gwamna kuma jigon siyasa, Sule Lamido,
- Malam Idris Muhammad, a madadin ɗaruruwan masu sauya shekar ya ce sun yi haka ne saboda ganin ayyukan ci gaban da APC ta kawo
- Ɗan Sule Lamiso, watau Mustapha Sule Lamido ne ke neman zama gwamnan Jigawa a inuwar PDP a zaben da ke tafe
Jigawa - Mambobin jam'iyyar PDP 200 sun sauya sheƙa zuwa jan'iyyar APC a ƙauyen Dagwaji dake Gundumar Kiyako, ƙaramar hukumar Birnin Kudu, jihar Jigawa.
Tribune ta tattaro cewa mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Birnin Kudu, Alhaji Yusuf Isa Wurno, ne ya karɓi masu sauya shekar a kauyen Dagwaji.
Da yake karɓan tuban sabbin mambobin APC, mataimakin Ciyaman ya tabbatar masu da cewa za'a ba su dama kamar ta kowa kuma za'a tafi da su a harkokin gudanar da jam'iyya.
Alhaji Yusuf Isa Wurno ya kuma ta ya su murnar shiga APC, inda ya ƙara da cewa, "Kun yanke hukunci cikin wayewa kuma a lokacin da ya dace, ina ƙara tama ku murna."
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya roki sabbin mambobin su maida hankali su yi aiki tukuru domin tabbatar da nasarar jam'iyyar APC a zaɓe mai zuwa.
A jawabin maraba, shugaban APC na gundumar Kiyako, Malam Ibrahim Shehu, ya yi kira tare da roko ga sauran magoya bayan wasu jam'iyyu da su taho su shiga APC idan cigaban mutane suke so.
Meyasa mutanen suka zabi koma wa APC?
Da yake tsokaci a madadin ɗaruruwan masu sauya shekan, Malam Idris Muhammad, ya ce sun yanke shawarin shiga APC ne saboda ɗumbin ayyukan ci gaban da ta kawo a jihar Jigawa.
Legit.ng Hausa ta gano cewa tsohon gwamnan jihar, Sule Lamido, ya fito daga wannan yankin na ƙaramar hukumar Birnin Kudu.
Matsala a Gidan Kwankwaso, Ɗan Takarar Mataimakin Gwamna Ya Yi Murabus
A wani labarin kuma Ɗan takarar mataimakin gwamnan jihar Neja a inuwar NNPP ta Kwankwaso ya yi murabus
John Bahago, wanda ya gode wa shugabannin NNPP da suka goya masa baya har ya kai wanan matakin, ya ce ya bar jam'iyyar baki ɗaya.
A wasikar da ya aike wa shugaban NNPP na gundumarsa, Bahago bai faɗi dalilin ɗaukar wannan mataki ba.
Asali: Legit.ng