Muna Aiki Tukuru Don Tabbatar da Tinubu Ya Zama Magajinka, Gwamnoni Ga Buhari

Muna Aiki Tukuru Don Tabbatar da Tinubu Ya Zama Magajinka, Gwamnoni Ga Buhari

  • Gwamnonin jam'iyyar APC sun tama shugaban ƙasa, Muhammasu Buhaɗri, murnar ƙarin shekara ranar Asabar
  • A ranar 17 ga watan Disamba, 2022, mai girma shugaban kasa ya cika shekaru 80 cif a duniya
  • A sakon ta ya shugaban murnar wannan rana, gwamnonin sun faɗi shirinsu kan ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu

Abuja - Ƙungiyar gwamnoni ci gaba na jam'iyyar APC sun ce suna aiki ba dare ba rana don tabbatar da Bola Tinubu, ɗan takarar shugaban kasa a inuwar jam'iyya mai mulki ya lashe zaɓen 2023.

Jaridar The Cable ta rahoto cewa sun faɗi haka ne a wata sanarwa da shugaban gwamnonin APC kuma gwamnan Kebbi, Atiku Bagudu ya fitar ranar Asabar.

Gwamnonin cigaba na jam'iyyar APC.
Muna Aiki Tukuru Don Tabbatar da Tinubu Ya Zama Magajinka, Gwamnoni Ga Buhari Hoto: thecable
Asali: UGC

Gwamna Bagudu, yace "Salon mulkin" shugaban kasa, Muhammadu Buhari ne asalin dalilin da ya jawo jam'iyyar APC ta ƙara karbuwa a zukatan 'yan Najeriya.

Kara karanta wannan

2023: Matar Atiku Abubakar Ta Girgiza Intanet, Ta Yi Subutar Bakin Da Ya Zarce Na Tinubu, Bidiyo

Ya kara da cewa gwamnonin APC na aiki tukuru don tabbatar da nasarar tsohon gwamnan jihar Legas a babban zaɓen 2023 mai zuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A sanarwar, wacce suka aike wa Buhari don taya shi murnar cika shekaru 80, Bagudu ya ce:

"Ƙungiyar gwamnonin cigaba na ta ya shugaban kasa, Muhammadu Buhari, kwamandan askarawan Najeriya, iyalansa da abokanansa murnar cika shekara 80. Ƙasa na murnar wannan rana ta musamman."
"Mun yaba da salon murkinka, manufofinka da sadaukarwarka wajen ɗaga darajar kasar nan. Shugabanni da mambobin APC sun yaba da mulkinka abin koyi."

Abinda gwamnonin suka faɗa wa Buhari game da Tinubu

Vanguard tace Bayan taya shugaban kasa murna, gwamnonin jam'iyyar APC sun kuma ba shi tabbacin cewa suna kan aiki da ji ba gani don nasarar Bola Tinubu a 2023.

"Yayin da muke tama ka murnar karin shekara da gode maka bisa aiki babu son kai ga ƙasar mu, muna jaddada maka kudirinmu na aiki ba kama hannun yaro don nasarar 'yan takarar APC a 2023."

Kara karanta wannan

2023: "Ka Ci Zaɓe Ka Ci Zabe" Yadda Dubun Dubatar Magoya Baya Suka Yi Maraba da Tinubu a Jihar Arewa

"Muna aiki tukuri kan doka da tsari domin tabbatar da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ɗan takarar mu na shugaban ƙasa ya samu nasara kuma ya zama magajinka."

A wani labarin kuma Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilar yace 'yan Najeriya sun sami sabon Buhari a jikin Bola Tinubu

Alhassan Ado Doguwa ya bayyana cewa babu maraba tsakanin shugaba Buhari da ɗan takarar shugaban kasa a APC, Bola Tinubu, wurin aiki ga al'umma.

Ɗan majalisar wakilan tarayya yace zangon mulki biyu ko shekara 8 kaɗai sun yi kaɗan jam'iyyar APC ta iya gyara ɓarnar jam'iyyar PDP tsawon shekara 16.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262