Matan Arewa Na Siyar Da Katunan Zabensu Kan N2000, Dattawan Arewa Sun Koka
- Kungiyar dattawan arewa sun zargi wasu yan siyasa da kokarin murkushe kuri'u a yankin arewacin kasar
- A cewar dattawan arewar, an gudanar da bincike don sanin matakin barnar da ake aikatawa
- Sun yi kira ga mutanen arewa kan kada su baiwa kowa katunan zabensu duk rintsi duk wuya
Kungiyar dattawan arewa ta koka kan cewa wasu yan siyasa na amfani da damar talaucin da ke addabar mutane a yankin arewa musamman mata wajen siye katunan zabensu.
A cewar dattawan, hakan wani yunkuri ne na murkushe yawan kuri'u a yankin arewacin kasar.
Daraktan labarai na kungiyar dattawan arewa, Dr Hakeem Baba-Ahmed ne ya bayyana hakan a wata hira da Channels Tv.
Kungiyar ta NEF ta yi ikirarin cewa an tursasa miliyoyin yan arewa musamman mata sakin katunan zabensu kan kudi N2,000, jaridar Vanguard ta rahoto.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya ce:
"Kungiyar dattawan arewa ta bi wannan al'amari mai cike da damuwa, tana shawartan shugabannin garuruwa da manyan masu ruwa da tsaki kan hatsarin da ke tattare da tauye hakkin yan kasa masu yawan gaske. Mun kuma gudanar da namu binciken, wanda yasa muka fito muka yi wannan gargadi.
"An sanya dubbai koma mai yiwuwa miliyoyin masu zabe a arewa musamman mata sakin katunan zabensu saboda na goro, a yawan lokuta wanda bai fi N2000 ba.
"A wasu lokutan ana fada masu cewa za a dawo masu da katunansu bayan an gama sarrafadu don biyan karin kudi a matsayin na rage radadin talauci. Ba a dawo da kowani katu. Bincikenmu ya nuna cewa wannan yunkuri na rage karfin kuri'un arewa."
Dalilin da yasa mutane ke siyar da kuri'unsu kan N2000
A cewar dattawan, mutanen da ke aikata wannan ta'asa suna yiwa jam'iyyun siyasa daban-daban aiki.
Kungiyar ta kuma bayyana cewa suna harin garuruwan da suke ganin jam'iyyunsu ko yan takararsu basu da tasiri sosai.
Dattawan arewan sun kuma koka kan halin talauci da ya mamaye arewa, suna masu cewa wannan na daga cikin abubuwan da suka haddasa hakan.
Hakeem Baba-Ahmed: Abun da zai sa na marawa Peter Obi baya
A wani labarin, kakakin kungiyar dattawan arewa, Hakeem Baba-Ahmed yace zai iya goyon bayan takarar Peter Obi idan har su suka fi dacewa don gaje Shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2023.
Asali: Legit.ng