2023: Kana Cikin Yan Takara Biyu Na Sahun Gaba Dake Neman Gaje Buhari, Soludo Ga Atiku

2023: Kana Cikin Yan Takara Biyu Na Sahun Gaba Dake Neman Gaje Buhari, Soludo Ga Atiku

  • Gwamnan Anambra ya kara jaddada matsayarsa cewa mutum biyu ne ke neman zama shugaban kasa dagaske a 2023
  • A makonnin da suka shige, Chukwuma Soludo, ya yi ikirarin cewa ba ya ga waɗan nan biyun sauran duk 'yan ta yi daɗi ne
  • Atiku Abubakar ya ziyarci gwamnan har gidan gwamnati sa'ilin da jirgin yakinsa ya dira Anambra ranar Alhamis

Anambra - Gwamna Chukwuma Soludo na jihar Anambra ya ayyana Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP a matsayin ɗaya daga cikin manyan 'yan takara biyu na sahun gaba a zaɓen 2023.

Channels tv tace Gwamnan ya yi wannan furucin ne a gidan gwamnatinsa da ke Awaka, ranar Alhamis lokacin da Atiku ya kai masa ziyara kafin zuwa filin kamfe.

Atiku da gwamna Soludo.
2023: Kana Cikin Yan Takara Biyu Na Sahun Gaba Dake Neman Gaje Buhari, Soludo Ga Atiku Hoto: @atiku
Asali: Twitter

"Kana ɗaya daga cikin manyan 'yan takara biyu da ake ganin su ne a sahun gaba a fafutukar ɗarewa mulkin Najeriya," inji gwamnan, tsohon shugaban babban bankin Najeriya (CBN).

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Majalisar Dattawa Ta Tabbatar da Sabbin Mataimakan Gwamnan CBN Biyu da Buhari Ya Naɗa

A 'yan makonnin ɗa suka shige, an ji gwamna Soludo na cewa mutum biyu ne kadai ke neman zama shugaban kasa a 2023, kuma ya kira sauran da, "yan wasan kwaikwayo."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Maganar gaskiya mai ɗaci da wahalar faɗa (wasu zasu ce Allah ya kyauta) ita ce mutum biyu ne ko jam'iyyu biyu ne su ke neman kujarar shugaban kasa dagaske, sauran yan dirama ɓe kawai masu ba da nishaɗi."

- Inji Soludo a wani dogon rubutu da ya wallafa a watan Nuwamba.

Jihata tana maraba da kowane ɗan takara - Soludo

Da yake maraba da Atiku, gwamnan ya kara da cewa Najeriya babbar ƙasa ce domin a wurinsa, "Allah ne ya kaddara zaman Najeriya ƙasa mai faɗi kuma mafi ƙarfi a nahiyar bakaken fata."

"Kofar Anambra a bude take ga kowane ɗan takara da zai zo kuma ya faɗa wa mutane tanadin da ya masu gabanin zaɓen 2023. Abinda mike so a ba kowa fili ya taka irin rawarsa."

Kara karanta wannan

Yan Najeriya Sun Samu Sabon Sumfurin Shugaba Buhari, Doguwa Ya Jaddada Wanda Ya Dace da Mulki a 2023

A nasa ɓangaren, ɗan takarar shugaban kasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar, ya ɗaukar wa mutanen Anambra muhimman alƙawurra musamman abinda ya shafi zaizayar ƙasa.

A wani labarin kuma Mai Magana da yawun ƙungiyar Dattawan Arewa yace abu ɗaya ne kacal zai sa ya marawa takarar Peter Obi baya a 2023

Ƙanin Hakeem Baba-Ahmed watau Datti Baba Ahmed ne ɗan takarar mataimakin Peter Obi na jam'iyyar Labour Party a zaɓen 2023.

Sai dai yace duk na ƙaninsa ne abokin takarar Obi, ba zai goyi bayansu ba har kwamitin ƙungiyoyin manyna arewa sun yanke cewa su ne suka fi cancanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262